Matsayin tsarkake ayyukan ibada don Allah a Musulunci (7)

Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jinkai. Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah, Ubangijin halittu. Tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabinmu, Bawan Allah Muhammad, tare da alayensa da sahabbansa baki daya da kuma duk wanda ya shiryu da shiriyarsa, ya siffatu da sunnarsa, har zuwa Ranar Sakamako.  Bayan haka, mu nan […]

Matsayin tsarkake ayyukan ibada don Allah a Musulunci (7)
Matsayin tsarkake ayyukan ibada don Allah a Musulunci (7)

Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jinkai. Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah, Ubangijin halittu. Tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabinmu, Bawan Allah Muhammad, tare da alayensa da sahabbansa baki daya da kuma duk wanda ya shiryu da shiriyarsa, ya siffatu da sunnarsa, har zuwa Ranar Sakamako. 

Bayan haka, mu nan dai a kan sinadarai ko makaman da ake tunkude Shaidan da su wajen tabbatar da ikhlasi a cikin ayyukan ibada. Mun gangaro tun daga cewa mutum ya kasance yana addu’a; yana boye aikin a inda ya kamata a boye; yana duban ayyukan magabata; yana raina ayyukansa; yana tsoron ko ba a karba masa ayyukan ba; rashin tasirantuwa da maganar mutane game da ayyukan; sannan yana sane da cewa mutane ba su da Aljanna balle wuta, balle su yi masa sakamako ko ukuba da dayansu ba; to yau kuma za mu ga na karshe, sannan mu ci gaba:
8. Tunanin kana cikin kabari tilonka:
Rai yana yin kyau, ya gyaru saboda tunani a kan makomarsa. Idan bawa ya hakkake a ransa cewa za a cusa shi a cikin kabari, shi kadai dinsa (tilonsa), ba tare da kowa ba, kuma ya yi yakinin ba wani abin da zai amfane shi ban da aikinsa na kwarai; kuma lallai dukkan mutanen duniya ba za su iya dauke masa komai ba na azabar kabari; sannan kuma (ya fahimci) dukkan al’amurra a Hannun Allah kadai suke; to a wannan lokaci ne zai tabbatar da yakinin cewa babu abin da zai kubutar da shi, sai ikhlasin aikin ibada ga Wanda Ya halicce shi, Shi kadai, Mai girma da daukaka (Allah ke nan).
Malam Ibnul kayyim, (Allah Ya jikansa), a cikin littafin dariikul Hijrataini, a shafi na 297, yana cewa, “Gaskiyar kwadaituwa wajen saduwa da Allah, yana daga cikin mafi amfanin abin da ke wajen bawa, kuma shi ne abin da ya fi kaiwa matuka wajen tabbatar da tsayuwarsa da kafuwarsa kan ibadarsa. Yadda al’amari yake ma dai shi ne duk wanda yake tattali don saduwa da Allah, to zuciyarsa za ta yanke daga duniya da duk abin da ke cikinta da ma duk wata hada-hadar nemanta.”
Wannan shi ne sinadari ko makamin karshe daga cikin jerin sinadaran, wadanda ake tu’ammali da su wajen tunkude Shaidan don tabbatar da tsarkakar niyyar aikin ibada (ikhlasi) don Allah kadai. Sai mu yi ta rokon Allah Ya tabbatar da duga-duganmu wajen gudanar da ayyukan ibada dominSa Shi kadai. Allah Ya sa mu dace!
Shin riya takan shigar wa salihan bayi?
Mashigar Shaidan a kan bawa tana da yawa. Yana shiga dukkan yanayin da mutane suke shiga cikinsa; kamar yana tunkuda ’yan kasuwa su rika cin riba a kasuwancinsu; yana kawata wa mata al’amurran kwalliya, wadanda aka haramta; kuma yana shigar wa salihan bayin Allah ta kofar riya.
Malam dibiy, (Allah Ya jikansa), ya ce, game da riya, “Ita ce mafi cutarwar hila (yaudara) ga rai, kuma mafi boyuwar makirce-makircenta; ana jarrabar malamai (masu ilimi) da ita da masu bautar Allah da masu gwagwarmaya wajen bin tafarkin Lahira.”
Ita riya ita ce mafi boyuwar kofofi (wadanda akan shige su ma ba a ankara ba), kuma mafi cutarwa ga bayin Allah.
An fadi, a cikin littafin tafsirin Taisiril Azizil Hamiid, shafi na 354, cewa, “Riya ta fi ban tsoro ga salihan bayin Allah a kan fitinar Dajjal.” Wato ba sa tsoron fitar Dajjal kamar yadda suke tsoron shigar riya a cikin ayyukansu na ibada. Allah Ya tsare mu!
Kuma lallai Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya kasance yana tsoronta (riya) a kan sahabbansa, domin yana ce musu, “Shin ba na ba ku labari ba, a kan abin da yake mafi tsoratarwar abin da nake tsoronsa a kanku fiye da Almasihud Dajjal?” Suka ce, “Muna son ji.” Ya ce, “Shirka boyayya (ko mai sauki ko karama). Mutum zai tsaya Sallah, ya kyautata ta, saboda abin da ya lura cewa wani yana kallonsa.” Imam Ahmad ne ya ruwaito shi. Wato mutum zai kawata sallarsa, ya kyautata yin ta, ba don Allah ba, sai don ya fahimci wani yana kallonsa kawai, don ya burge shi. Shi salihin bawa, idan ya yi aikin ibada don wani ya gani ya yaba masa (riya), to ana azabtar da shi, a Ranar Lahira, kafin waninsa. Wato shi ne farkon wanda za a fara azabtarwa kafin kowa.
Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), yana cewa, “Na farko cikin mutane da za a fara yanke wa hukunci a Ranar Lahira, shi ne mutumin da ya yi shahada (aka kashe a wajen yakin daukaka kalmar Allah – Jihadi). Sai a zo da shi, a nuna masa ni’imar da aka tattala masa, sai ya gane ta, sai Allah Ya ce, “Me ka aikata domin samunta?” Sai ya ce, “Na yi yaki dominKa, har sai da na yi shahada (aka kashe ni).” Sai Ya ce, “Ka yi karya. Sai dai kai ka yi yakin ne domin a ce maka jarumi, kuma an fadi hakan.” Daga nan sai a yi umarnin a ja shi a kan fuskarsa har sai an jefa shi a wuta. Sai kuma mutumin da ya yi ilimi kuma ya karantar da ilimin nasa, kuma ya karanta Alkur’ani. Sai a zo da shi, a nuna masa ni’imar da aka tattala masa domin haka, sai ya gane ta, sai Allah Ya ce, “Me ka aikata domin samunta?” Sai ya ce, “Na yi ilimi kuma na karantar da ilimin, kuma na karanta Alkur’ani dominKa.” Sai Ya ce, “Ka yi karya. Sai dai kai ka yi ilimi ne domin a ce maka malami, kuma an fadi hakan, kuma ka karanta Alkur’ani domin a ce kai makaranci ne, kuma an fadi haka din.” Sai a yi umarnin a ja shi a kan fuskarsa har sai an jefa shi a wuta. Sannan sai mutumin da Allah Ya yalwata masa kuma ya ba shi dukiya mai yawa, sai a zo da shi, a nuna masa ni’imar da aka tattala masa, sai ya gane ta, sai Allah Ya ce, “Me ka aikata domin samunta?” Sai ya ce, “Ban bar wata hanya, wadda Kake son a ciyar a kanta ba, face sai da na ciyar dominKa da dukiyata. Sai Ya ce, “Ka yi karya. Sai dai kai ka aikata haka ne domin a ce kai mai kyauta ne, kuma an ce haka din. Shi ke nan sai a yi umarnin a ja shi a kan fuskarsa har sai an jefa shi a wuta.” Muslim ne ya ruwaito Hadisin.
Ka yi tunani da dubi na hankali a kan wannan Hadisi, sai ka gane cewa farkon wanda za a yanke wa hukunci a Ranar Lahira a tsakanin mutane, shi ne mai jihadi da malami da mai sadaka da dukiyarsa, dukkansu kuwa hakan tana faruwa gare su ne idan niyyarsu da baci dangane da aikin ibadar da suka gudanar. Saboda haka, sai a ja su a kan fuskokinsu har cikin wuta, duk da kasancewar ayyukan da suka aikata suna daga cikin mafi girman ayyukan ibada a wajen Allah, sai dai juyar da niyya daga barin ikhlasi ta tunkuda su cikin wutar Hawiyah! Allah Ya tsare mu.
Mu kwana nan, sai mako na gaba, in Allah Ya kai mu. Allah Ya taimaki wannan sabuwar gwamnati da aka rantsar a yau. Allah Ya fisshe ta kunyar alkawurran da ta yi wa al’ummar Najeriya. Wassalamu alaikum warahmatullahi wa barakatuh!