Matsayin yi wa Allah godiya a Musulunci (1)

Gabatarwa Bayan haka, ya ku al’ummar Musulmi da ’yan Najeriya! Allah Ya yi baiwa da yawa ga bayinSa. Hannun damarsa kulllum cikin kyauta yake dare da rana. Yana bayar da kyautarSa ga wanda Ya so ba tare da lissafi ba. Yakan jarrabi wasu bayinSa da alheri iri-iri kamar yadda Yake jarraba su da sharri da […]

Matsayin yi wa Allah godiya a Musulunci (1)
Matsayin yi wa Allah godiya a Musulunci (1)

Gabatarwa

Bayan haka, ya ku al’ummar Musulmi da ’yan Najeriya! Allah Ya yi baiwa da yawa ga bayinSa. Hannun damarsa kulllum cikin kyauta yake dare da rana. Yana bayar da kyautarSa ga wanda Ya so ba tare da lissafi ba. Yakan jarrabi wasu bayinSa da alheri iri-iri kamar yadda Yake jarraba su da sharri da bala’o’i. Allah Madaukaki Ya ce: “Kuma Muna jarraba ku da sharri da alheri domin fitina. Kuma zuwa gare Mu ake mayar da ku.” (k:21:35).
Allah Yakan bayar da alheri duk da wadannan, kuma jarrabawar jin dadin rayuwa ta fi tsanani a kan ta lokacin wahala, sai dai abin da zai zamo mafi alfanu shi ne a kasance masu hakuri da kuma nuna godiya.
Talauci da dukiya dukkan su hanoyoi ne na jarrabawa, don haka ya wajaba ga mutum ya kasance mai hakuri da godiya ga Allah a cikin dukkan al’amuran da Ya yi umarni ko Ya hana da kuma dukkan abubuwan da Ya kaddara. Hakuri yana ginuwa ne a kan wadannan abubuwa biyu. Allah Ya hada godiya da imani lokacin da Ya ce: “Mene ne Allah zai amfana da yi muku azaba idan kun gode, kuma kuka yi imani?” (k:4:147).
Allah Madaukaki Ya gaya mana cewa nuna godiya gare Shi, shi ne makasudin halittarmu. Ya ce: “Kuma Allah ne Ya fitar da ku daga cikkunan iyayenku, ba da kuna sanin komai ba, kuma Ya sanya muku ji da gannai da zukata, tsammaninku za ku gode.” (k:16:78).
Kuma Ya ce Yana jin dadi tare da yarda kan gode maSa: “Kuma idan kun gode, zai yarda da ita (godiyar) a gare ku.” (k:39:7).
Kuma Ya halicci dare da yini ne don a yi tunani kuma a gode maSa: (Kuma Shi ne Wanda Ya sanya dare da yini a kan mayewa ga wanda yake son ya yi tunani ko kuwa ya yi nufin ya gode.” (k:25:62). Kuma Ya rarraba bayinSa zuwa gida biyu: Masu godiya da marasa godiya, sai Ya ce: “Lallai ne Mu, Mun shiryar da shi ga hanyar kwarai, ko ya zama mai godiya, ko kuma ya zama mai butulci.” (k:76:3). Kuma Allah Ya nuna Yana daukar masu gode maSa a matsayin masu bauta maSa, wadanda kuma ba su gode maSa ba su cikin masu bauta maSa. Ya ce: “Kuma ku gode wa Allah, idan kun kasance Shi kuke bauta wa.” (k:2:172). Sannan Ya yabi Manzo na farko da Ya aiko duniya cikin fadinSa: “Zuriyar wadanda Muka dauka tare da Nuhu. Lallai ne shi ya kasance wani bawa mai yawan godiya.” (k:17:3).
Kuma Ya umarci Annabi Musa ya karbi annabta da sako da wahayin da ke tare da shi da godiyar Allah. “Ya ce: “Ya Musa! Lallai ne Ni, Na zabe ka bisa ga mutane da manzanciNa, kuma da maganaTa. Saboda haka ka riki abin da Na ba ka, kuma ka kasance daga masu godiya.” (k:7:144).
Kuma ya yabi badadayinSa Annabi Ibrahim (AS) saboda shi mai godiya ne. Sai Ya ce: “Lallai ne Ibrahim ya kasance shugaba, mai kaskantar da kai ga Allah, mai karkata zuwa gaskiya, kuma bai kasance daga masu shirki ba. Mai godiya ne ga ni’imominSa (Allah), Ya zabe shi, kuma Ya shiryar da shi zuwa ga tafarki madaidaici.” (k:16:120-121).
Kuma Ya umarci Annabi Dawuda kan ya kasance mai godiya gare Shi. Ya ce: “Ku aikata godiya ya ’ya’yan Dawuda kuma kadan ne mai godiya daga bayiNa.” (k:34:13). Kuma Ya gaya mana cewa Annabi Sulaiman ya ce: “Ya Ubangijina Ka cusa min in gode wa ni’imarKa, wadda Ka ni’imta ta a gare ni da kuma ga mahaifana biyu…” (k:27:19).
Kuma Allah wasiyya ta farko da Allah Ya yi ga mutum ita ce ya gode maSa, sa’annan ya gode wa iyayensa, inda Ya ce: “Kuma Mun yi wasiyya ga mutum game da mahaifansa biyu; uwarsa ta dauke shi a cikin rauni a kan wani rauni, kuma yayensa a cikin shekara biyu (Muka ce masa), Ka gode Mini da kuma mahaifanka biyu, Makoma zuwa gare Ni kawai take.” (k:31:14).
Haka kuma Annabawa sun umarci mutanensu kan su rika gode wa Allah. Annabi Ibrahim (AS) ya ce da mutanensa: ““Saboda haka ku nemi arziki a wurin Allah kawai, kuma ku bauta maSa, kuma ku yi godiya zuwa gare Shi…” (k:29:17).
’Yan uwa Musulmi! Babu wanda yake daukar darasi daga ayoyin Allah sai mai godiya ga Allah: “Kamar wannan ne Muke sarrafa ayoyi domin mutane wadanda suke godewa.” (k:7:58). Yin godiya ga Allah na daya daga cikin abubuwan da Annabi (SAW) ya yi wasiyya ga sahabbansa. Ya ce da Mu’az: “Ya kai Mu’az! Ina sonka. Don haka kada ka daina fadi a karshen kowace Sallah. “Allahumma a’inni ala zikrika wa shukrika wa husni ibadatika – ma’ana “Ya Ubangiji! Ka taimake ni wajen ambatonka da yi maKa godiya da kyautata bauta gare Ka.”
Ibnu Taimiyya ya ce: “Na yi nazari kan addu’o’i mafiya kyau, sai nag a ita ce: “Allahumma a inni ala zikrika wa shukrika wa husni ibadatika.”
A lokacin da Shaidan makiyin Allah ya san cewa matsayi mafi girma da nuna godiya ga Allah ke kaiwa, kuma shi ne magi girman aikin ibada, sai ya rika kokarin hana mutane daga aikata hakan. Allah Madaukaki Ya ce: “Sa’an nan kuma hakika ina je musu daga gaba gare su, kuma daga baya gare su, kuma daga barin jihohin damansu da barin jihohin hagunsu: Kuma ba za Ka samu mafi yawansu masu godiya ba.” (k:7:17).
Manzonmu (SAW) ya kasance mafi godiyar mutane ga Allah Ubangijin. Ya bar duniya a lokacin da ko gurasarsa bai ci ba. Wani lokaci yakan dora dutse a kan cikinsa saboda yunwa. Alhali an gafarta masa abin da ya gabata da abin da ya jinkirta na zunubinsa. Yakan tashi ya rika sallolin nafila cikin dare har kafofinsa su rika kumbura, amma duk da haka idan aka yi masa magana sai ya ce: “Ashe b azan zama bawa mai godiya ba?”
Yi wa Allah godiya har wa yau yakan kawo kubuta daga azaba. Allah Madaukaki Ya ce: “Mene ne Allah zai amfana da yi muku azaba idan kun gode, kuma kun yi Imani?” (k:4:147). Kuma an tserar da Annabi Ludu ne daga azaba saboda godiyarsa ga Allah. Allah Ya ce a cikin littafinsa: “Lallai Mun aika iskar tsakuwa a kansu, face mabiyan Ludu, Mun tsirar da su a lokacin asuba. Saboda wata ni’ima daga gare Mu. Kamar haka Muke saka wa wanda ya gode.” (k:54:34-35).
Lokacin da mutanen Saba’i suka nuna rashin godiya ga Allah suka saba masa sai Allah Ya dire albarkarSa daga gare su suka dandani azaba. Kuma a cikin Suratul kalam da ma’abuta lambu suka ki godiya ga Allah kan ni’imarSa da nuna rowa ga matalauta sai Allah Ya kone lambun ko gonar.
Fudailu bin Iyal ya ce: “Ka gode wa Allah a koyaushe kan falala da rahamarSa domin da yawa baiwa da falalar Allah kan dawo ga mutanen da aka raba su da ita.”
Ya ’yan uwana masu girma! Duk wata baiwa da ba za ta kusanta mutum da Allah ba, babu shakka fitina ce. Yi wa Allah godiya na tsare baiwar da ake da ita kuma ta dawo da wadda aka rasa.