Matsin Rayuwa: Gwamnoni da Sarakuna na ganawa a fadar shugaban ƙasa

A halin yanzu babu wata sanarwa a hukumance game da maƙasudin gudanar da taron.

Matsin Rayuwa: Gwamnoni da Sarakuna na ganawa a fadar shugaban ƙasa

Gwamnoni da Sarakuna na gudanar da wani muhimmin taro yanzu haka a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.

Sai dai ba a bayyana maƙasudin gudanar da taron ba a hukumance.

Wasu majiyoyi sun ce shugannin na tattauna ne kan matsalolin da suka addabi Najeriya, tare da lalubo hanyoyin rage wahalhalun da jama’a ke fuskanta.

Aminiya ta ruwaito cewa gwamnonin na neman shawarwari daga sarakunan gargajiya domin taimaka musu wajen tsara manufofi da yanke shawara da za su amfani ’yan Najeriya baki ɗaya.

Daga cikin gwamnonin da suka halarci taron akwai Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Najeriya, Abdulrahman Abdulrazak (Kwara), tare da Sheriff Oborevwori (Delta), Dapo Abiodun (Ogun).

Sauran sun haɗa da Seyi Makinde (Oyo), Agbu Kefas (Taraba), Muhammad Inuwa Yahaya (Gombe) da kuma Uba Sani (Kaduna).

Wasu daga cikin manyan sarakunan gargajiya da suka halarci taron, sun haɗa da Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, Oni na Ife, Adeyeye Enitan Ogunwusi, da Etsu Nupe, Yahaya Abubakar.