Matsin rayuwa: Makaho mai shekara 65 ya sa a jefa shi a teku

An ceto wani makaho mai shekaru 65 a lokacin da yake ƙoƙarin faɗawa a cikin teku da nufin kashe kansa a Jihar Legas.

Matsin rayuwa: Makaho mai shekara 65 ya sa a jefa shi a teku

An ceto wani makaho mai shekaru 65 a lokacin da yake ƙoƙarin faɗawa a cikin teku da nufin kashe kansa a Jihar Legas.

An ceto dattijon ne a kan Gadar 3rd Mainland, zai faɗa a cikin take, saboda rashin iya ɗaukar nauyin iyalinsa.

Dattijon ya tafi gadar ne tare da ’ya’yansa biyu maza masu shekaru 12 da kuma 16, wadanda ya umarce su da jefo shi a tekun.

Yaran suna ƙoƙarin jefa mahaifin nasu ne wani mutum ya hango su, aka ceto dattijon.

Da aka bincika abin da ke faruwa, sai makahon ya bayyana cewa ’ya’yansa ne kuma shi ne ya ba su umarnin yin hakan, saboda tsananin ƙuncin rayuwa da talauci da yake ciki.

Kwamishinan ’yan sanda a Jihar Legas, Benjamin Hundeyin, ya ce a ranar Alhamis aka ga mutumin da ’ya’yan nasa za su jefa shi a tekun, aka sanar da ’yan sanda.

“Mutumin ya  bayyana cewa ya yanke shawarar halaka kansa ne saboda gwamnati ta riƙa kulawa da ’ya’yan nasa bayan rasuwarsa,” in ji Hundeyin.

A cewar jami’in, hukuma tana ƙoƙarin tuntubar matar makahon da kuma tallafa wa iyalan.

An kama bokaye 2 kan zargin yi wa shugaban Zambiya asiri

Kirsimeti: FRSC ta aike jami’ai 1,539 zuwa Kano

Gwamnatin Kano na shirin tara harajin 80bn a 2025

Kirsimeti: Zulum ya ɗauki nauyin jigilar fasinjoji 710 zuwa garuruwansu