Matsin rayuwa ya sa Magidanci rataye kansa a Jigawa
Wani magidanci ya rataye kansa saboda tsadar rayuwa da matsanancin talauci a Jihar Jigawa.
Wani magidanci ya rataye kansa har lahira saboda tsadar rayuwa da matsanancin talaucin da suka addabe shi a Jihar Jigawa.
Shiisu ya bayyana cewa da misalin karfe 11 na daren ranar Alhamis ne rundunar ‘yan sandan jihar ta samu mummunan labarin.
Ya ce jami’an rundunar ne suka kwance gawar magidancin daga cikin bishiyar da aka gano ta a rataye, suka kai ta asibiti domin gudanar da bincike
DSP Shiisu ya bayyana cewa rundunar ta samu labarin cewa tun ranar Laraba da ta gabata magidancin ya fice daga gidansa ba tare da an san inda ya tafi ba, sai daga bisani a gano gawarsa rataye a jikin bishiyar.
A cewarsa bincike ya nuna magidancin ne ya rataye kansa da kansa, saboda matsin rayuwa da tsananin talauci da suka sa shi gaba.