Matsin tattalin arziki ya shafi duniya ne ba Najeriya kadai ba – Babangida Aliyu

Tsohon Gwamnan Jihar Neja, kuma Shugaban Gidauniyar Tunawa da Sardauna, Alhaji Mu’azu Babangida Aliyu, ya bukaci ’yan Najeriya su yi hakuri kan matsin tattalin arzikin da ake fuskanta a kasar nan, inda ya ce ba a Najeriya kadai ba ce duk duniya ne.Alhaji Babangida Aliyu ya bayyana haka ne a lokacin da jami’an Gidauniyar Sardauna […]

Matsin tattalin arziki ya shafi duniya ne ba Najeriya kadai ba – Babangida Aliyu
Matsin tattalin arziki ya shafi duniya ne ba Najeriya kadai ba – Babangida Aliyu

Tsohon Gwamnan Jihar Neja, kuma Shugaban Gidauniyar Tunawa da Sardauna, Alhaji Mu’azu Babangida Aliyu, ya bukaci ’yan Najeriya su yi hakuri kan matsin tattalin arzikin da ake fuskanta a kasar nan, inda ya ce ba a Najeriya kadai ba ce duk duniya ne.
Alhaji Babangida Aliyu ya bayyana haka ne a lokacin da jami’an Gidauniyar Sardauna suka kai ziyarar jaje ga gwamnati da al’ummar Jihar Borno tare da mika tallafin ga ’yan gudun hijirar Boko Haram, a karshen makon jiya.
Dokta Mu’azu Babangida Aliyu ya ce, “Mutane da yawa ba su san cewa ba Najeriya kadai ke cikin wannan hali ba duk duniya ne abin ya shafa. Idan aka lura a yanzu a duk duniya an shiga fadi-tashi ne, kuma an taba shiga irin wannan tsanani daga shekara ta 2008-2009, amma da yake lokacin man fetur yana da daraja sosai sai ya zamo ba mu ji shi sosai ba. Yanzu farashin man ya fadi kasa warwas, kuma abubuwan da aka rika ganowa na badakalar da wadansu suka yi na cewa wadansu suna ta rabon kudin kasa ba mu sani ba da sauransu, sun taimaka wajen tsaurarawa da kuma kuncin da jama’a muka shiga. Ina ganin ya kamata a sashi a kundin tsarin mulkin Najeriya cewa kowace jam’iyya ta sa batun yaki da cin hanci da rashawa ya zama babban kudirinta domin a rika bin ka’idoji wajen gudanar da al’amura.”
Babangida Aliyu ya kara da cewa, shawara dai ita ce dole wanda yake gwamnati ya yi kokarin kwatanta adalci kan yadda zai kula da talakawansa su kuma talakawa su yi ta yi wa shugabanni addu’a da biyayya. “Idan irin wannan abin ya faru, sai mutum ya rage hannu, idan kana kashe Naira 100 kan wani abin jin dadi da bai zama dole ba, sai ka rage zuwa Naira 30 ko 40. Wato idan a da kana shan ruwan gora 10 ne sai ka dawo 4 ko 5 kuma muna tsammanin wannan tsanani na dan lokaci ne Allah zai kawo karshensa,” inji shi.
Dokta Babangida Aliyu, ya nuna bakin ciki game da bala’in da yakin Boko Haram ya sanya Jihar Borno da yankin Arewa maso Gabas a ciki. “Wannan yanki na Arewa maso Gabas, musamman Jihar Borno ya gamu da bala’in rasa rayukan akalla mutum dubu 20, da raba wajen mutum miliyan biyu da muhallansu, a wannan yaki na Boko Haram, don haka ya zama dole mu zo mu jajanta wa’yan uwanmu mu taya su bakin ciki, kuma muna rokon Allah Ya kawar da wannan abu cikin gaggawa,” inji shi.