Matuƙin jirgi ya mutu ana tsaka da tafiya a sararin samaniya

Wani matuƙin jirgin sama ya rasu a yayin da suke tsaka da tafiya a sararin samaniya.

Matuƙin jirgi ya mutu ana tsaka da tafiya a sararin samaniya

Wani matuƙin jirgin sama ya rasu a yayin da suke tsaka da tafiya a sararin samaniya a hanyar zuwa ƙasar Turkiyya.

Matuƙin jirgin kamfanin Turkish Airlines ya yanke jiki ya ce ga garinku ne bayan sun tashi daga birnin Saetle da ke Yammacin ƙasar Amurka.

Wannan lamari ya sa abokan aikinsa yin saukar gaggawa da jirgin a New York, ranar Talata bayan duk kokarinsu na farfaɗo da shi ya faskara.

Kakakin kamfanin, Yahya Ustun ya sanar a ranar Laraba cewa matuƙin jirgin ya rasu ne a hanyarsu ta zuwa birnin Samtanbul na kasar Turkiyya.

Ya ce,  “matuƙin ƙirar Airbus 350… mai lamaba TK204 daga Seattle zuwa Samtanbul ya rasu ne a yayin da ake a sararin samaniya.”

“Bayan abokan aikinsa sun yi, sun yi su farfaɗo da su sun kasa, suka yi saukar gaggawa, amma kafin su sauka rai ya yi halinsa.”

Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito Mista Ustum yana cewa mamamcin mai shekaru 59 ya fara da aiki a kamfanin ne a shekarar 2007, kuma lafiyarsa ƙalau kafin ya gamu da ajalinsa.