Matuka jiragen sama za su fara yajin aiki
Matuka jirgin sama sun ba da sai biyu a dawo da takwarorinsu da aka kora daga aiki da sunan matsin COVID-19 ko su yi yajin aiki. Kungiyar matuka da injiniyoyin jirgin sama (NAAPE) ta yi kashedin ga kamfanonin jiragen sama da suka ko suke shirin sallamar ma’aikata. Bayan sallamar ma’aikatan guda 170 da kamfanonin Air […]
Matuka jirgin sama sun ba da sai biyu a dawo da takwarorinsu da aka kora daga aiki da sunan matsin COVID-19 ko su yi yajin aiki.
Kungiyar matuka da injiniyoyin jirgin sama (NAAPE) ta yi kashedin ga kamfanonin jiragen sama da suka ko suke shirin sallamar ma’aikata.
Bayan sallamar ma’aikatan guda 170 da kamfanonin Air Peace da Bristow suka yi a cikin makon nan, kungiyar ta ce dole a dawo da su.
Shugaban kungiyar na kasa Abednego Galadinma ya ce rashin dawo da su zai sa kungiyar ta tsayar da bangaren jiragen sama a fadin Najeriya.
Galadinma ya soki kamfanin helikwafta na Bristow bisa sallamar matuka jirgi guda 100 bisa hujjanr matsin COVID-19.
Ya ce kamfanin ya yi aiki babu tsaiko a lokacin kull inda ya yi wa kamfanonin mai da sauran muhimman bangarori jigila.
NAAPE ta bukaci Hukumar Sufurin Jiragen Sama ta Najeriya (NCAA) ta gaggauta hana kamfanonin korar matuka da injiniyoyin jiragen.
“Su gaggauta dawo da matauka jirgi da injiniyoyin da suka kora har sai an cika dukkannin dokokin kwadago ko NCAA ta rufe su, saboda mummuna abin da hakan zai haifar”, inji shi.
“Wannan karya dokar da kuma yadda muke kishin ‘yan uwanmu, zai haifar da rikici idan har ba a yi abun da muke so ba an da sati biyu.
“Zai zama ba mu da zabi face matuka jirgi da injiniyoyi a dukkannin kamfanonin jirage su tsunduma yajin aiki,” inji shi.
Shugaban na NAAPE ya yi watsi da sanarwar Bristow na cewa matuka jirgi da injiniyoyi 100 da za ta sallama har da ‘yan kasashen waje.
Galadinma ya ce hakan wata dabara ce da kamfanin ke son yin amfani da ita ya yi waje da ‘yan Najeriya.
“Cewa ba ‘yan kungiyarmu ba ne kadai matuka jirgi da injiniyoyi 100 da za a kora magana ce mara makama domin ba da mu aka yi ta ba.
“Mu samman Bristow, sun mayar da ‘yan kungiyarmu masu zaman banza duk da tabbacin gwamnati na tallafa musu domin kar su kori ma’aikata.
“Yanzu haka kamfanonin ba su da isassun ma’aikata, kuma yawancin ma’aikatan nasu ma ‘yan kasashen waje ne.
Amma suna neman korar ma’aikata ba tare da mutunta dokar kayyade rabon aiki tsakanin ‘yan kasa da baki ba, da sunan COVID-19.
“Su daina fakewa da COVID-19 saboda rufe tashoshin jirgi bai shafi ayyuka irin na kamfanonin mai ba. Sannan Bristow da Caverton sun yi aiki a lokacin kulle.
“In ba ku manta ba, ‘ya’yan kungiyarmu ne Gwamnatin Jihar Ribas a tsare, saboda haka kar su ce za su kafa hujja da COVID-19.
“Bristow ya yi aiki a tsawon lokacin kulle, inda gwamnati ta ba shi ayyukan mai da iskar gas; amma za su zo suna neman fakewa da COVID-19 su sallami takwarorinmu”, inji kungiyar.