Matukin jirgi

Wani matukin jirgi ne ya dauki wasu mahaukata a cikin jirgin sama, daya daga cikinsu kuwa yana kusa da shi a yayin da yake tuka su. Shi wannan mahaukaci, ana tsammanin ya kusa warkewa, ya fi sauran hankali. Suna tsakar tafiya, sai sauran mahaukatan suka yi ta kara da surutu mai yawa. Ganin haka sai […]

Matukin jirgi
Matukin jirgi

Wani matukin jirgi ne ya dauki wasu mahaukata a cikin jirgin sama, daya daga cikinsu kuwa yana kusa da shi a yayin da yake tuka su. Shi wannan mahaukaci, ana tsammanin ya kusa warkewa, ya fi sauran hankali. Suna tsakar tafiya, sai sauran mahaukatan suka yi ta kara da surutu mai yawa. Ganin haka sai matukin jirgin ya ce wa wanda ya kusa warkewa: “Ka je ka tsawata musu, su daina surutu, sun dame mu haka nan.” Shi kuwa ya amsa, ya tashi ya tafi. Jim kadan sai ga shi ya dawo ya zauna, ya ce: “Haba, ka ji wurin duk ya yi tsit!” Da direba ya tambaye shi dalili, sai ya ce: “Ai da na ce musu su yi shiru suka kiya, sai na bude kofar jirgin nan, na ce duk wanda ba zai shiru ba ya fita. Shi ne suka yi ta fita daya bayan daya har suka kare!”
Daga Shehu Lawal Tsafe 08091573703

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno