Matukin jirgin saman Etihad ya mutu a bakin aiki

Matukin Jirgin saman Etihad da ya tashi daga Abu Dhabi zuwa Amsterdam ya mutu a bakin aikinsa, al’amarin da ya haifar wa jirgin saukar gaugawa a kasar Kuwait. A sanarwar da kamfanin jirgin saman ya bayar a Abu Dhabi ya je wannan babban jirgin jigilar kaya an karkatar da akalar tafiyarsa ne zuwa Kuwait, inda […]

Matukin jirgin saman Etihad ya mutu a bakin aiki

Matukin Jirgin saman Etihad da ya tashi daga Abu Dhabi zuwa Amsterdam ya mutu a bakin aikinsa, al’amarin da ya haifar wa jirgin saukar gaugawa a kasar Kuwait.

A sanarwar da kamfanin jirgin saman ya bayar a Abu Dhabi ya je wannan babban jirgin jigilar kaya an karkatar da akalar tafiyarsa ne zuwa Kuwait, inda ya sauka lafiya kuma jami’an kula da lafiya suka taru a kansa, wadanda suka tabbatar da mutuwar matukin.

“Kamfanin sufurin jiragen sama na Etihad Airways ya nuna bakin cikinsa kan rasuwar daya daga cikin matukan jirginsa samfurin EY 927, mai jigilar kaya daga abu Dhabi zuwa Amsterdam, bayan da matukin ya samu lalurar rashin lafiya a farkon tashinsa, sai abokin aikinsa ya aike da sakon neman daukin gaugawa, har ya samu saukar da jirgin a kasar Kuwait kamar yadda yake kunshe a sanarwar Etihad.