Mauldi kwaikwayon Kiristoci ne – Bin Usman
Aminiya ta kuma tattauna da Sheikh Bin Usman, wani fitaccen Malamin Musulunci da ke Kano game da bikin Maulidi, kuma ga yadda tattaunawar ta kasance: Sheikh, mene ne matsayin mauludi a Musulunci? A gaskiya mauludi bidi’a ne kai-tsaye saboda Manzon Allah (SAW) bai yi ba, sahabbansa masu tsarki ba su yi ba. Wadansu ne […]
Sheikh Muhammad Bin Usman
Aminiya ta kuma tattauna da Sheikh Bin Usman, wani fitaccen Malamin Musulunci da ke Kano game da bikin Maulidi, kuma ga yadda tattaunawar ta kasance:
Sheikh, mene ne matsayin mauludi a Musulunci?
A gaskiya mauludi bidi’a ne kai-tsaye saboda Manzon Allah (SAW) bai yi ba, sahabbansa masu tsarki ba su yi ba. Wadansu ne suka kirkire shi bayan shekara 400 da barin Annabi (SAW) duniya. Manzon Allah ya bayyana cewa duk wanda ya farar da wani abu a cikin addini, wanda ban yi ba sahabbaina ba su yi ba, to wannan abin juyarwa ne, ma’ana an maida masa abinsa. Mauludi ba ya cikin Musulunci, kirkira ce. Wanin Sarki ne ya kirkire shi mai suna Abu Sa’id Alkaukabi. Idan mun duba shi ya fi Ananbi (SAW) sanin kansa da kansa ne ko kuma ya fi Sayyidina Abubakar da Umar da Usman da Ali (Allah Ya yarda da su? Gaskiya daya ce, mauludi sankara ce a cikinsa. Matsayinmu ke nan kuma dole mu gaya wa jama’a gaskiyar lamari.
Ba ka ganin mauludi yana nuna karfin Musulunci ne, kamar yadda ake fada?
Ta yaya za a yi a ce mauludi yana nuna karfin Musulunci, abin da Annabi (SAW) bai yi ba, sahabbansa ba su yi ba? Ke nan Annabi (SAW) bai san abin da ke nuna karfin Musulunci ba sai wani daga baya? Idan ka ce yana nuna karfin Musuunci sai mu ce ta wace fuska? To me ye sa Allah bai ce a yi ba? Yaya Manzon Allah (SAW) bai yi ba? Sayyidina Abubakar ya yi shekara biyu da wata uku da kwana 10 yana Khalifa amma bai yi ba. Wato shi bai san karfin Musulunci ba? Sayyidina Umar ma da ya zo bai yi ba, shi ma bai san karfin Musulunci ba? Sayyidina Usman ya yi shekara 11 da wata 11 da kwana 11 a kan gadon Khalifanci amma bai yi ba, shi ma bai san karfin Musulunci ba? Shi ma Sayyidina Ali da ya hau Khalifanci, ya yi shekara hudu da wani abu kuma bai yi ba. Sai bayan shekara 400 da wafatin Ananbi (SAW) sannan wadansu suka kirkiro, wanda suna kwaikwayon Kirista ne. Sun ce tunda Kirista na yi, su ma za su yi wa Ananbi (SAW).
Karfin Musulunci na cikin bin abin da Annabi (SAW) ya kawo. Ga duk wanda ba ya da son zuciya, babu batun karfin Musulunci cikin bidi’a; karfin Musulunci na cikin bin abin da Ananbi (SAW) ya kawo. Idan ka kawo ra’ayinka, na kawo nawa, abin da muke cewa shi ne akwai abin da Manzon Allah (SAW) ya kamata ya fadi kuma bai fadi ba sai muka gani a yanzu. Mauludi ba ya nuna karfin Musulunci sai dai ya kawo wa Musulunci rauni. Wa ke cewa Sallah a rana ba biyar ba ce, bai ishe mu karfi ba? Abubuwa daruruwa ba su ishe mu karfi ba, sai an kawo abin da Annabi (SAW) bai yi ba?
Ba ka ganin mauludi yana hada kan Musulmi?
Wanann tambayar ’yar uwar ta baya ce. Mauludi ba ya hada kan Musulmi sai dai ma ya jawo wa Musulmi farraka. Asalin masu janyo farraka tsakanin Musulmi su ne masu cewa abin da Annabi (SAW) ya yi ba daidai ba ne, koda ba su fadi da bakinsu ba amma su shigo da son zuciyarsu, maimakon a bi abin yadda yake. Ta wace fuska mauludi yake hada kan Musulmi? Idan Alkur’ani da Hadisi ba su hada kan Musulmi ba, to Ya Ilahi me zai hada kanmu? Misali kamar mutum ne ya zo ya ce Najeriyar nan ba daya ba ce, biyu ce, ya haifar da rikici. Sai aka ce ku da kuka ce Najeriya daya ce ku hakura a tafi a kan cewa biyun ce, wannan shi ne hadin kai, anya hankali zai kama wannan? Abu ne kawai da mutum ya kirkiro yake neman me zai gaya wa mabiya don ya samu goyon baya, sai a fadi wancan, a fadi wancan. Ita gaskiya ba ta bukatar ado. Ita Sunnah da gaskiya kamar zuma ne, ba su bukatar talla, madi ne ke bukatar talla. To tallar bidi’ar ake so a yi wa mutane. Dadinta shi ne jama’a sun yi karatu yanzu, an riga an gane, an yi gaba.