Maulidi na haɗa kan al’umma – Sarkin Agege

Sarkin Hausawan Agege, Alhaji Muhammadu Musa  Dogonkaɗe ya bayyana cewa taron bikin tunawa da ranar  haihuwar Manzon Allah (saw) a matsayin harsashin sada zumunci a tsakanin al’ummar Musulmi tare da haɗa kansu. “Idan ana maganar maulidi, abu ne da ya shafi Musulmin duniya gaba ɗaya. Taruwarmu a nan don gabatar da maulidi, tunawa ne da […]

Maulidi na haɗa kan al’umma – Sarkin Agege

Sarkin Hausawan Agege, Alhaji Muhammadu Musa  Dogonkaɗe ya bayyana cewa taron bikin tunawa da ranar  haihuwar Manzon Allah (saw) a matsayin harsashin sada zumunci a tsakanin al’ummar Musulmi tare da haɗa kansu. “Idan ana maganar maulidi, abu ne da ya shafi Musulmin duniya gaba ɗaya. Taruwarmu a nan don gabatar da maulidi, tunawa ne da tarin alheran da Annabi Muhammadu (saw) ya zo mana da su kuma wannan abu ne da ya kamata ce ba sai shekara ba kawai. Don haka ne a ɗariƙarmu ta Tijjaniyya muke da tsare-tsare da dama domin tunatar da mu Allah da manzonSa a kowane lokaci. Haka wannan taro da muke duk shekara, muna yinsa ne domin janyo hankalin Musulmin duniya game da muhimmancin wannan rana ta haihuwar fiyayyen halitta. Mu kuma yi haƙuri da juna, mu zamo tsintsiya ɗaya maɗaurinki ɗaya kamar yadda Annabi ya koya mana,” inji shi.

Sarkin ya shaida haka ne a yayin ƙaddamar da zagayen maulidi na bana, wanda ya gudana a ranar Lahadin da ta gabata. Maulidin kuma ya sami halartar Shugaban karamar Hukumar Agege Alhaji Abdulganiyu Kola Egunjobi da wasu muƙƙaraban Gwamnatin jihar Legas.

Babban Sakataren kungiyar Majma’u Ahbabu Rasulullah, wace ita ce ta assasa zagayen maulidi a Jihar Legas, Malam Musa Ado ya shaida wa Aminiya cewa suna gudanar da zagayen maulidin ne a duk shekara cikin tsari da bin doka. “Yau kimanin shekara 8 ke nan da muka fara zagayen maulidi a Legas kuma mana yinsa ne bisa bin doka da tsari, domin mukan nemi izinin Gwamnatin Jihar Legas, sannan muna yin aikin ne da taimakon jami’an tsaro na ’yan sanda da soji da jami’an tsaro na asiri, da ma hukumar kiyaye haɗɗura da ba da agajin gaggawa. A wannan zagaye da muka yi na bana, mun yi rijistar aƙalla mutum dubu 7 ban da waɗanda suka shiga aka yi da su, waɗanda ba su yi rijista ba. Akwai tarin makarantun Isalamiya da ƙungiyoyi da suka shigo daga ciki da wajan Legas, suka zo aka yi da su kuma alhamdu lillahi, an yi zagayen an gama lafiya,” inji shi.

Masu zagayen maulidin, mazansu da matansu da yara ƙanana sun yi  zagayen manyan titunan birnin Legas, inda suka fara daga harabar fadar Sarkin Hausawan Agege. Zagayen ya ƙunshi makarantu na ƙabilun Yarabawa da Hausawa da sauran ƙabilun yankin.