Maulidi: Obaseki ya taya Musulman Edo murna

Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki ya ja hankalin Musulman jihar a kan su ci gaba da koyi da kyawawan halayen Annabi Muhammad (S.A.W). Obaseki ya bayyana haka ne cikin jawabin taya murnar zagayowar ranar haihuwar fiyayyen halitta Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallam da ya ke gudana a ranar Alhamis. Maulidi: Gwamnati ta ba da hutu […]

Maulidi: Obaseki ya taya Musulman Edo murna

Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki ya ja hankalin Musulman jihar a kan su ci gaba da koyi da kyawawan halayen Annabi Muhammad (S.A.W).

Obaseki ya bayyana haka ne cikin jawabin taya murnar zagayowar ranar haihuwar fiyayyen halitta Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallam da ya ke gudana a ranar Alhamis.

Obaseki ya ce, “Ina taya Musulmai maza da mata na jihar Edo da ma kasa baki daya murnar zagayowar ranar haihuwar Annabi Muhammad (S.A.W).

“A wannan rana muna kira da Musulmai mu ci gaba da nuna kauna da zaman lafiya, domin cigaban jiharmu da kasa baki daya”, inji shi.

Ya kuma yi kira gare su da su ci gaba da zama makwabta nagari kamar yadda Ma’aikin ya koyar.

Daga nan sai ya yi kiran samun hadin kan mutanen jihar domin wanzuwar zaman lafiya.

Boko Haram sun ƙone makarantu a Borno

Har yanzu ’yan bindiga ba su saki matar Manjo Janar Rabe ba

An binne gawar Manjo Janar Rabe a Katsina

Wasu tsiraru ne ke rura matsalar tsaro a Najeriya — Christopher Musa