Maulidin Duniya na gobe a Kebbi na nan daram – Alkasim Yawuri
Babban Sakataren Jam’iyyatu Ansaruddeen Attijaniya, Muhammad Alkasim Yahaya ya ce Mauludin Duniya da Shehu Ibrahim Inyas ya kafa da za a yi a Birnin Kebbi yana nan daram ba a daga shi ba kamar yadda wadansu ke rade-radi. Alkasim Yawuri, ya bayyana haka ne a yayin tattanawa da manema labarai a jiya Alhamis a Birnin […]
Alkasim Yawuri
Babban Sakataren Jam’iyyatu Ansaruddeen Attijaniya, Muhammad Alkasim Yahaya ya ce Mauludin Duniya da Shehu Ibrahim Inyas ya kafa da za a yi a Birnin Kebbi yana nan daram ba a daga shi ba kamar yadda wadansu ke rade-radi.
Alkasim Yawuri, ya bayyana haka ne a yayin tattanawa da manema labarai a jiya Alhamis a Birnin Kebbi, inda ya ce taron mauludin wanda shi ne irinsa na farko da aka taba yi a tarihin Tijjaniyya a kasar nan, zai samu halartar manyan malamai daga sassan duniya da suka hada da Murtaniya da Masar da Senigal da sauransu.
Ya ce “Wannan taro ba a daga shi ba, yana nan wanda za a tattauna rayuwar Manzon Allah (SAW) da kuma ainihin soyayyar Manzon Allah, domin soyayyar Annabi ita ce gari a Musulunci, tana sama da komai. Kuma wannan taro za mu iya cewa wata babbar jami’a ce za mu bude ta soyayyar Manzon Allah, domin za mu yi kwana biyu, daga Alhamis zuwa Asabar a Birnin Kebbi.”