Mauludi: Ganduje ya raba wa Malaman darika 110 shanu da shinkafa
Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje, ya raba wa Malaman Darikun Sufaye 110 shanu da buhunan shinkafa da kudin cefanen Maulidi. Ganduje ya ce gwamnati ta bayar da kayan abincin ne saboda jama’a su samu damar gudanar da Maulidi cikin walwala da jin dadi. Ganduje ya dawo da Salihu Tanko bakin aikinsa An kama ’yan Najeriya […]
Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje, ya raba wa Malaman Darikun Sufaye 110 shanu da buhunan shinkafa da kudin cefanen Maulidi.
Ganduje ya ce gwamnati ta bayar da kayan abincin ne saboda jama’a su samu damar gudanar da Maulidi cikin walwala da jin dadi.
- Ganduje ya dawo da Salihu Tanko bakin aikinsa
- An kama ’yan Najeriya da suka kwace jirgin Birtaniya
- Buhari ya yi ganawar sirri da TY Danjuma
Shugaban Karamar Hukumar Nassarawa, Lamin Sani Kawaji ne ya wakilci gwamna wurin raba kayan abincin.
Lamin, ya ce Gwamnatin Kano na raba kayan abincin a kowace shekara don taimaka wa jama’ar Kano su yi shagalin Maulidin Annabi Muhammad (SAW) cikin yanayin farin ciki.
A jawabin da ya gabatar a madadin sauran malaman da suka sami tallafin kayan abincin, Dakta Kamaluddini Adamu Na Ma’aji ya ba wa gwamnan tabbacin amfani da kayan abincin ta hanyar da ta dace.
Sauran kayan da aka raba wa zawiyoyin sun hada da ruwan sha da robobin zuba abinci da kuma littattafan Tarihin Annabi Muhammad (SAW).