Mauludin Nyass: An yi canjaras tsakanin taron Abuja da na Kaduna

A ranar Asabar da ta gabata ce mabiya darikar Tijjaniya wadda daya ce daga cikin darikun Sufaye da Sidi Ahmad Tijjani ya assasa a shekarar 1784 a Aljeriya kuma daya daga cikin darikun Musulunci da ke da mafi yawan mabiya a Afirka ta Yamma suka gudanar da Mauludin mutum na biyu mafi daraja a darikar […]

Mauludin Nyass: An yi canjaras tsakanin taron Abuja da na Kaduna

A ranar Asabar da ta gabata ce mabiya darikar Tijjaniya wadda daya ce daga cikin darikun Sufaye da Sidi Ahmad Tijjani ya assasa a shekarar 1784 a Aljeriya kuma daya daga cikin darikun Musulunci da ke da mafi yawan mabiya a Afirka ta Yamma suka gudanar da Mauludin mutum na biyu mafi daraja a darikar Sheikh Ibrahim Nyass.

Mabiya darikar suna daukar Sheikh Ibrahim Nyass Khaulaha, Sahibul Faidha a matsayin mujaddadin darikar inda suke yin Mauludinsa duk shekara. Sai dai a bana an samu matsala kan inda za a gudanar da Mauludinsa wanda shi ne karo na 32, kuma ya dace da cikarsa shekara 118 da haihuwa. An haife shi ne a ranar 15 ga Rajab, 1398 Bayan Hijira, daidai da 8 ga Nuwamban 1900. 

Yadda takaddamar ta faro

Masu lura da al’amura suna ganin gogoriyon nuna karfi da yawan mabiya da ke akwai a tsakanin fitaccen malamin addinin Musuluncin nan kuma jagora a darikar Sheikh dahiru Usman Bauchi da kuma Halifan Tijjaniya, Sheikh Isyaka Rabi’u da ta faro shekaru da dama ce ta jawo rarrabuwar kawunan mabiya darikar har ta kai ga yin Mauludin na Nyass a Abuja da Kaduna, maimakon yi a wuri daya da aka saba.

A wata ganawa da manema labarai a makon jiya Sheikh dahiru Bauchi ya bayyana cewa Maulidin da za a yi na bana ya samu wani irin salo ne, saboda da farko mutanen Taraba ne suka nemi a gudanar a jiharsu, amma saboda rashin zaman lafiya suka ce bai kamata a yi wani abu na biki a Taraba ba, “Sai muka daga, sai mutanen Kaduna suka ce suna so a yi musu Maulidin a Kaduna, sai muka karba to muna cikin wannan hali sai mutane suka kawo shawara, suka kawo hujjoji gamsassu suka ce su sun fi so a yi maulidin a Abuja, sai muka amsa muna cikin wannan sai mutanenmu na Kaulaha shi ainihin Khalifanmu na Kaulaha Magajin Shehun, Shehu Tijjani (RA) bai tilasta a yi a Kaduna ko Abuja ba. Ana cikin wannan hali, sai abin ya zama kamar Shehu din ne yake so ya nuna bunkasarsa cewa yana so a yi Maulidin fiye da na kullum,” inji Shehin.

Sheikh dahiru Bauchi, wanda ya yi ta kokarin nuna ba baraka aka samu ba, ya kara cewa: “Wadansu samari ne suka sa wani abu da ba a ji dadinsa ba, shi ko lamarin ba na yara ba ne ba na samari ba ne, lamari ne na Khalifofin Shehu da Khalifan Shehu, ba yadda za a yi wani almajirin Shehu ya yi jayayya da Khalifan Shehu na Kaulaha abu ne da ba zai yiwu ba don mu shi abin girmamawa ne a wajenmu, dan Shehu wanda ya zama Khalifa mu abin girmamawa ne a gare mu ba abin jayayya ba ne. Saboda haka har yanzu dai wadansu suna cewa za a yi a Abuja wadansu suna cewa za a yi a Kaduna, abin ba na jayayya ba ne ba na gaba ba ne, kafin lokacin ya iso dai za mu san yadda za mu yi, tunda abin na bayyana soyayya ga Shehu Ibrahim ne.”

Sai dai ga duk mai bibiyar lamarin zai fahimci takaddamar da ta taba tasowa lokcin da aka bayyana Sheikh Isyaka Rabi’u a matsayin Halifan Tijjaniyya wanda Sheikh dahiru Bauchi ya nuna ja da hakan daga farko har ya kai ga darewar kungiyar agaji ta Fityanul Islam gida biyu, ita ce ta ci gaba da taka rawa wajen farraka mabiya Tijjaniyya ’yan Faidah a wannan karo.

Muhawara ta yi zafi

Duk wanda yake bibiyar shafin facebook mai suna: “2018 Mauludin Shehu Ibrahim INyass a Kaduna State.” zai ga yadda ’yan Failah mabiya darikar suka rika jefa wa juna maganganu domin tabbatar da sun kare gwaninsu a muhawarar da suka rika yi.

Misali a ranar 21 ga Fabrairu, 2018 shafin ya buga wata sanarwa mai kanun “Breaking News Kaduna State 14/04/18” dauke da sanya hannun Sheikh Sani Rogo da Sayyadi Sani Zubairu masu magana da yawun kungiyar Majma’u Ahbab Sheikh Ibrahim Inyass (RTA) Association of Nigeria, inda suka ce ranar 14 ga Afrilun bana ce ranar Maulidin Sheikh Alhaji Ibrahim Nyass, kuma a Jihar Kaduna za a yi.

Sannan ranar 24 ga Maris, shafin ya buga wani rubutu mai taken “A Kaduna za a yi Mauludin Sheikh Ibrahim Nyass ba a Abuja ba, inji Sheikh Tijjani Abdulkadir Zariya.

A cikin rubutun Shehin Malamin ya nemi a yi watsi da abin da ya kira jita-jitar cewa ba a Kaduna za a yi Mauludin Nyass ba, inda a karshe ya ce:  “Ko muryar wa aka ji ya bayyana cewa ba a Kaduna za a gudanar ba, kada a yarda da shi.”

Kuma a ranar 2 ga Afrilu sai ga wani bayani a wannan shafi mai taken: ‘Mauludin Shehu na kasa 2018’ inda aka ruwaito cewa “Tawagar Lisanul Faidha Maulana Sheikh dahiru Usman Bauchi (RTA) a karkashin jagoranci da wakilcin, Assayyid Alhaji Ibrahim bin Maulana Sheikh dahiru Usman Bauchi (RTA) sun kai ziyara ta musamman ga Khadimul kur’an, Maulana Sheikh Ishaka Rabi’u (RTA) domin tattaunawa a kan mas’alar Mauludin Shehu. Ana matukar kyautata zato a wannan zama cikin ikon Allah za a yi amfani da shawarar da wasikar Sheikh Tijjani Niasse (RTA) domin zartar da garin da za a yi Mauludin Shehu a tarayyance, domin a guje wa farraka.

Kwamtsam ranar 4 ga Afrilu, sai ga wani bayani a shafin daga Majma’u Ahbab Sheikh Ibrahim Nyass mai taken: “Hakikanin gaskiyar magana a kan ziyarar da Sayyadi Alhaji Ibrahim ya kai wa Maulana Khalifah Sheikh Ishaka Rabi’u (RTA) a gidansa.” Marubutan sun ce “Muna sanar da ’yan uwa Ahlullahi cewa maganar da ake yadawa a kan an yi zama a gidan Khalifah don tsida waje guda da za a yi Maulidin Shehu, to ’yan uwa wannan magana ba gaskiya ba ce.”

kungiyar ta ce, Sayyadi Alhaji Ibrahima Sheikh dahiru Bauchi (RTA) ya je ne ya tuba a kan abin da ya aikata na raba kan muridan Shehu wanda ya yi nadamar aikatawa a kan a yafe shi, kuma Khalifah Sheikh Isyaka Rabi’u ya ce masa ya karbi tubarsa. Kuma Khalifah ya ce masa wannan laifi ba shi kadai aka yi wa ba saboda haka ya tafi Khaulaha “Wajen Maulanmu Khalifatul Amm, Shehu Tijjani (RTA) ya nemi gafara kuma ya gaya masa cewa sun janye maganar Maulidin Abuja.” 

kungiyar ta hannun masu magana da yawunta ta ce, Maulidin Shehu na kasa da Majma’u Ahbab Sheikh Ibrahim Inyass (RTA) ta saba shiryawa yana nan a Kaduna ranar 14/04/18 za a yi insha Allah! 

Sannan a ranar 6 ga Afrilu, 2018 wani ya tura wani rubutu mai taken “Raba Gardama,” inda a ciki ya ce Shehu Tijjani Nyass ya tabbatar da Kaduna a matsayin wurin da za a yi Mauludin Nyass na bana. 

Shehu Tijjani Nyass ya raba gardama:

A ranar 8 ga Afrilu, 2018, wani ya sake tura wani bayani a shafin mai taken “Warwarar Ishkali Cikin Sha’anin Mauludin Shehu.” Wannan rubutu ya nuna yadda Khalifatul Amm, Shehu Tijjani Nyass ya raba wannan gardana ta amincewa a yi Mauludin a Kaduna da Abuja, kuma ya nuna shi kansa na Abujan zai je, inda Sheikh dahiru Bauchi zai kasance. Marubucin ya ce “Bayanai biyu sun riske mu, masu kamanceceniya da juna wajen jagora guda daya, a kan mas’alar garuruwan da za a yi Mauludin Shehu.”

Ya ce, “Bayani na farko da ya riske mu shi ne “Maulanmu Sheikh Tijjani Inyass (RTA) Ya ce “Sheikh dahiru Usman Bauchi (RTA) bai bukatuwa ga neman izini a wajensa, domin zartar da wani sha’ani na addini, kamar Mauludi. Kasancewarsa mai izini mudalaki daga Maulanmu Sheikh Ibrahim Inyass (RTA), zai iya yin mauludi a duk inda yake so a fadin duniya.”

Ya kara da cewa: “Sannan cikin sakon da ya aiko da Sayyadi Alhaji Ibrahim zuwa ga Khalifa Sheikh Isyaka Rabi’u (Rta) ya ce “Duk inda Sheikh dahiru Usman Bauchi (Rta) yake, shi ma a nan yake. Wadannan zantuka kai-tsaye nuni suke cewa “Khalifa Tijjani Inyass (RTA) ya amince da yin Mauludin Shehu a Abuja.”

Kuma ya ce: “Bayani na biyu da ya fito daga Maulana Khalifa Sheikh Tijjani Inyass (rta) shi ne zancensa na amincewa da yin Mauludin Shehu a garin Kaduna. Kasancewar Khalifa Tijjani Inyass (rta) malami ne na addini, mai koyi da Annabi (SAW) cikin zartar da abubuwansa cikin adalci. Hakan zai taimaka mana ainun wajen gano irin hikimar da ke cikin wannan hukunci nasa.”

Bayan kawo wasu nassoshi marubucin ya kare da cewa: “Idan muka dauki wannan al’amari muka auna shi da zancen Maulanmu, Khalifa Sheikh Tijjani Inyass (Rta) za mu gano cewa “Yin Mauludi a Abuja, umarninsa ne, kamar yadda zance ya gabata, hakazalika yin Mauludi a Kaduna shi ma zancensa ne. A takaice, wanda ya yi Mauludi a Abuja, soyayyarsa ga Shehu karbabbiya ce, Haka wanda ya yi Mauludin Shehu a Kaduna shi ma soyayyarsa ga Shehu karbabbiya ce, illa dai abin nema shi ne tsarkake niyya da ikhlasi. Kada halartar dayan wajen mauludan nan ya zamo sila da wani zai yi gaba da wani Batijjane dan uwansa, ko ya yi fada da shi, ko ya gaya masa mummunar magana, ko ya hantare shi, ko yake ganin shi ya fi dayan falala, tunda duk a kan manufa daya za a tafi wato “Godiya ga Allah bisa samuwar jagoran da ya zo mana da alherai da falaloli daga Allah da ManzonSa (SAW).

Komai ya tsaya cik a Abuja da Kaduna:

Daga Abbas Jimoh da Maryam Ahmadu-Suka

Wakilanmu da suka halarci wuraren Mauludan biyu, sun ruwaito cewa al’amura sun tsaya ciki a biranen Abuja da Kaduna a yayin gudanar da Mauludan biyu. 

A Abuja tsakiyar Birnin Abuja ya yi cikar kwari ta yadda komai ya tsaya cik na wuni biyu da aka dauka ana gudanar da Mauludin, inda mabiya darikar da suka fito daga jihohin kasar nan da kasashe 16 na Afirka da Turai suka hallara. An fara gudanar da Mauludin a Masallacin kasa, amma cinkoson jama’a ta tilasta mayar da shi zuwa Dandalin Eagles. Dandazon jama’a ta sanya hatta jami’an tsaro da masu kula da ababen hawa sun gaza yin komai, bayanai sun ce wadansu ma sun ajiye motocinsu ne a wajen Abuja da suka hada da garuruwan Deidie da ke da nisan kilomita fiye da 20 da Maraba a Jihar Nasarawa suka tako a kasa.

Sannan makarantu da filayen wasanni da gidajen mabiya darikar sun gaza daukar bakin ta yadda dubban mutane suka rika kwana a filin Allah.

A gefe guda kuma masu sayar da abinci da ruwan sha sun rika ci karensu babu babbaka suna yin muguwar tsada ga jama’ar da suka haralci Mauludin.

Khalifatul Amm na darikar Tijjaniyya Sheikh Tijjani Nyass daga Senegal da Sheikh dahiru Bauchi da Ministan Ilimi Malam Adamu Adamu wanda ya wakilci Shugaban kasa Muhammadu Buhari da wakilan gwamnonin jihohin Nasarawa da Neja da na Sarkin Musulmi da tsohon Shugaban Majalisar Wakilai Ghali Na’abba da tsohon Gwamnan Jihar Kano Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da sauransu da dama da kuma wakilai daga kasashen Moroko da Libya da Senegal da Tanzaniya da Masar da Birtaniya da Jamus da wasu kasashen Turai ne suka halarci Mauludin na Abuja wanda ya gudana cikin kwanciyar hankali.

A Kaduna inda aka gudanar da Mauludin a Dandalin Murtala an hadu da cinkoson jama’a sakamakon kwararar mabiya darika wadanda suka mamaye titunan Ali Akilu da Alkali Road da dukan wuraren da ke kewayen dandalin. Dandalin Murtala ya yi cikar kwari ta yadda akasarin wadanda suka halarci Mauludin suka kasace a wajensa.

A sakon Shugaban kasa Muhammadu Buhari da Minista Adamu Adamu da Ministan Harkokin Cikin Gida Laftana Janar Abdulrahman Dambazau suka gabatar a wajen Mauludan ya bukaci ’yan Najeriya su zauna lafiya da juna don ci gaban kasar nan. Ya yaba wa mabiya darikar Tijjaniyya kan shirya Mauludan da ya ce za su taimaka wajen karfafa soyayya da girmama juna a tsakanin mabiya, inda ya yi kira ga Musulmi su ci gaba da yi wa kasar nan addu’a tare da yin koyi da koyarwa marigayi Sheikh Nyass wanda ya yada addinin Musulunci ta hanyar nuna kauna da soyayya kuma ya isa ga dukan al’ummar duniya.

daya daga cikin jikokin Nyass, Sheikh Sharif Umar wanda ya halarci Mauludin na Kaduna ya nuna jin dadinsa kan dubban mutanen da suka halarci bikin.

Bakin da suka halarci Mauludin na Kaduna baya ga wadanda suka fito daga jihohin Najeriya, akwai wadanda suka zo daga kasashen Senegal da Nijar da Ghana, Kamaru da kuma Birtaniya.