Mauludin Nyass: Namadi ya bukaci a yi wa kasa addu’o’in zaman lafiya
Mataimakin Shugaban kasa Muhammad Namadi Sambo ya bukaci a ci gaba da yi wa kasar nan addu’o’i don dorewar zaman lafiya.Alhaji Namadi Sambo, ya yi wannan kira ne a Gombe a wurin Mauludin Sheikh Ibrahim Nyass karo na 28 da kuma cika shekara 114 da haihuwarsa.Mataimakin Shugaban kasar ya hori al’ummar Musulmi su dage wajen […]

Mataimakin Shugaban kasa Muhammad Namadi Sambo ya bukaci a ci gaba da yi wa kasar nan addu’o’i don dorewar zaman lafiya.
Alhaji Namadi Sambo, ya yi wannan kira ne a Gombe a wurin Mauludin Sheikh Ibrahim Nyass karo na 28 da kuma cika shekara 114 da haihuwarsa.
Mataimakin Shugaban kasar ya hori al’ummar Musulmi su dage wajen yi wa kasar addu’o’i saboda halin da ta tsinci kanta a ciki na rashin zaman lafiya da tsaro.
Ya ce taron mauludin da mabiya darikar Tijjaniya suka shirya ya nuna cewa Musulmi ’yan uwan juna ne kuma masu kaunar zaman lafiya ne da son jama’a a koyaushe.
A nasu jawaban Shugaban Majalisar Tarayya, Aminu Waziri Tambuwal da Gwamnan Jihar Gombe, Ibrahim Hassan dankwambo da Sheikh dahiru Usman Bauchi da kuma Sheikh Isiyaka Rabi’u da sauran shehunnai da suka fito daga kasashen duniya sun bukaci Musulmi mabiya darikar Tijjaniya su zama masu kaunar juna da rungumar kowa da kowa.
Khalifa Ahmadu Tijjani Nyass, dan marigayi Ibrahim Nyass bai yi wani jawabi ba, amma ya bayar da umurnin cewa a ci gaba da gudanar da addu’o’i na musamman don ganin an kawo karshen fadace-fadacen da ke faruwa a wasu kasashen duniya.
Wani jigon darikar Tijjaniya a Jihar Gombe kuma Halifan Sheikh Ahmadu Ngaudare Malam Yaya Ahmadu Ngaudare, nuna farin cikinsa ya yi kan yadda taron Maulidin ya gudana a Gombe cikin lumana ba tare da wata hayaniya ba.
Halifa Yaya Ahmadu Ngaudare, ya kuma yaba wa dukkan shehunnan darikar na jihar da na kasa da na Afirka da suka halarci taron maulidin Shiekh Ibrahim Nyass karo na 28
a Gombe, kuma wanda shi ne na cikar shekara 114 da haihuwar Nyass din.
Daga nan sai Malam Yaya Ngaudare, ya ce taron maulidin ya yi armashi yadda ya kamata, inda jama’a suka cika garin kuma babu wani wanda aka samu da nuna rashin bin doka kuma an yi taron lafiya an gama lafiya.
An haifi Sheikh Ibrahim Nyass ne a kasar Senegal a1900, shekara 114 da suka gabata kuma ya rasu ne a 1979.
Taron mauludin wanda ya gudana a babban filin wasa na tunawa da marigayi Sarkin
Gombe Abubakar Umar da ke kan hanyar Dukku, ya samu halartar shehunnai da zakirai da malamai da magoya bayan darikar Tijjaniya daga sassan kasar nan da kasashen Moroko da Aljeriya da Senega da sauransu.