Mawaƙin Hip Hop Lil Jon ya karɓi musulunci a Amurka

Lil Jon ya zama shahararren Ba’amurke na biyu da ya karɓi Musulunci a makon farko na Ramadan.

Mawaƙin Hip Hop Lil Jon ya karɓi musulunci a Amurka

Lil Jon

Fitaccen mawaƙi kuma furodusa, Jonathan H. Smith wanda aka fi sani da Lil Jon, ya karɓi addinin Musulunci a wani masallacin garin Culver da ke Jihar California a kasar Amurka.

Kafofin watsa labarai irinsu Daily Sabah da HipHopDx sun ruwaito cewa, a ranar Juma’a Lil Jon ya ziyarci masallacin Sarki Fahad da ke birnin Los Angeles inda ya bayyana cewa ya musulunta a gaban babban taron jama’a.

Wani faifan bidiyo da aka yada a shafukan sada zumunta ya nuna mawakin yana karanta shahada da larabci sannan da turanci, karkashin jagorancin limamin masallacin.

Lil Jon wanda aka haifa a shekarar 1972 a garin Atlanta na Jihar Jojiya, shahararren mawaƙin rap ne saboda rawar da ya taka a matsayin jagaba wajen haɓaka rukunin hip-hop a farkon shekarun 2000.

Lil Jon wanda ke da mabiya fiye da miliyan 1 a dandalan sada zumunta, a baya bayan nan ya sake daukar hankalin jama’a bayan fitowar kundin wakokinsa mai suna Meditation .

Bayan marubuci Ba’amurke kuma mai fafutuka Shaun King, Lil Jon ya zama shahararren Ba’amurke na biyu da ya karɓi Musulunci a makon farko na watan Ramadan.