Mawaka sun nuna rashin gamsuwa da kalankuwar Kaduna

Wasu mawaka da suka taimaka wa Jam’iyyar APC, wajen samun nasarar kafuwar gwamnatin Shugaban kasa Muhammad Buhari, sun koka kan yadda aka shirya taron gangamin mawakan jam’iyyar da aka gudanar a karshen makon jiya a garin Kaduna. Mawakan sun koka kan yadda aka shirya taron ne, a zantawarsu da wakilinmu a Jos, inda a cewar […]

Mawaka sun nuna rashin gamsuwa da kalankuwar Kaduna
Mawaka sun nuna rashin gamsuwa da kalankuwar Kaduna

Wasu mawaka da suka taimaka wa Jam’iyyar APC, wajen samun nasarar kafuwar gwamnatin Shugaban kasa Muhammad Buhari, sun koka kan yadda aka shirya taron gangamin mawakan jam’iyyar da aka gudanar a karshen makon jiya a garin Kaduna.
Mawakan sun koka kan yadda aka shirya taron ne, a zantawarsu da wakilinmu a Jos, inda a cewar wani mawaki, M.B. Musa Jos da ke zaune a garin Jos, ya ce ya je wajen kalankuwar kamar yadda aka gayyace shi, amma sai aka ce masa wai an canja sunayen da aka bayar da farko.
“Mu mun san mawakan da suka bai wa Jam’iyyar APC gudunmawa wajen samun nasarar wannan gwamnati, ta hanyar wake-waken da suka yi wa jam’iyyar. Amma sai aka zo aka dauki wasu mawaka, wadanda ba su yi komai ba, aka karrama su a wajen taron. Don haka ba mu ji dadin yadda aka shirya wannan taro ba,” inji shi.
Ya ce a Najeriya ni ne na fara sakin wata waka, a lokacin da aka ake tsakiyar fitar da sakamakon zaben Shugaban kasa Muhammad Buhari, mai suna: ‘Ku gaya musu mun lashe zabe.’ Haka kuma ya ce ya yi wata waka mai suna ‘APC babbar jam’iyya, kudu, yamma, arewa muna jira, zo Baba Buhari ka agaza, bana mai malafa zai je kasa.’
M.B. Musa ya ce ya yi wakoki da dama ga wannan jam’iyya, amma duk da wadannan wakoki sai ga abin da aka yi masa. Ya yi kira ga wadanda za su sake shirya irin wannan taro nan gaba, su tantance ainihin wadanda suka yi wa jam’iyyar waka, don ganin an karrama su, ba irin yadda aka yi a wajen wannan taro ba.
Shi ma a zantawarsa da wakilinmu, wani mawakin Jam’iyyar APC da ke zaune a Kano, Ikiram Kano, cewa ya yi wannan taro da aka shirya ba taron karrama mawakan Jam’iyyar APC ba ne. Ya ce a Najeriya, kusan kowa ya san wakar da ya yi wa Shugaban kasa Buhari, mai suna ‘Idan za a yi zabe a yi gaskiya, ba za mu yarda da rinto ba.’ Ya ce wannan waka ba biyansa aka yi ba, ya yi ta ne kawai don soyayya.
Ya ce: “Mun yi nasara sakamakon wadannan wakoki da muka yi amma abin takaici, ba a karrama mu ba a wajen wannan taro. Don haka a gaskiya ba mu ji dadin abin da aka yi mana ba a wajen taron.”
A zantawarsa da wakilinmu, wani mawakin Jam’iyyar APC da ke zaune a Jos, Murtala Mamsa, ya ce ya fara yi wa Shugaban kasa Muhammad Buhari wakoki tun daga Jam’iyyar ANPP zuwa CPC har zuwa wannan jam’iyya ta APC. Ya ce ya yi wa Shugaban kasa Muhammad Buhari wakoki sama da 15.
Ya ce a ranar da Shugaba Buhari ya kaddamar da fara yakin neman zabensa, a karkashin Jam’iyyar APC a Abuja, shi kadai aka ba dama ya yi waka a wajen. Ya ce amma abin takaici sai gashi ba a karrama shi ba a wajen taroN. “Don haka a gaskiya ba mu ji dadi ba, kan yadda aka shirya wannan taro,” inji shi.
A cewar Ahmed Abubakar Shanawa, mawakin Jam’iyyar APC a Jos: “Gaskiya muna da korafi kan yadda aka shirya wannan taro, musamman ganin yadda muka yi amfani da kudi da ilimi da lokacinmu, muka ba da gudunmawa wajen samun nasarar wannan gwamnati.”
Ya ce ya kashe kudi da dama wajen shirya wakokin Jam’iyyar APC da Shugaban kasa Muhammad Buhari waka don kishin kasa, domin a samu canji a cikin kasa. Ya ce ba na yi wadannan wakoki ne don in an kafa gwamnati a biya ni ba. “Amma tunda an waiwaiyo kan wannan sana’a, ya kamata a ce muna cikin wadanda aka karrama a wajen taron. Tunda an ce wannan taro na Najeriya ne baki daya, ya kamata a ce an dauko koda mutum daya ne daga kowace jiha a kasar nan. Domin akwai mawakan da suke tafiya da Shugaban kasa Buhari tun lokacin da ya fara gwagwarmayar neman Shugabancin kasar nan,” inji shi.
Shi ma a zantawarsa da wakilinmu, wani mawakin Shugaban kasa Buhari da ke garin Kano, Abdulrahman Ayuba Alfazazi, cewa ya yi: “Gaskiya na ji dadi da har aka dubi gudunmawar da muka bayar a wannan tafiya, har aka shirya wannan taro na garin Kaduna. Amma ina da korafi kan yadda na ga wasu mawaka da dama da suka ba da gudunmawarsu a wannan tafiya, babu sunayensu a cikin wadanda aka karrama a wajen taron. Ina kira ga Gwamnatin Jihar Kaduna kan ta binciki ’yan kwamitin da suka shirya taron, kan yadda suka gudanar da wannan aikin da aka ba su. Domin a gaskiya ba su yi abin da ya kamata ba, a aikin da aka ba su ba.”
Daga nan ya yi kira ga duk gwamnatin da za ta shirya irin wannan taro a nan gaba, kan ta dauki mutanen da suke da ruwa a wannan harka ta damka musu aikin, domin ganin an yi aikin yadda ya kamata.