Mawaka za su bunkasa in suna da abin da za a saurare su – Marlo King
Umar Abubakar Umar wanda aka fi sani da Marlo-King sanannen mawakin Hip-Hop ne da ke tashe a Jihar Kano. A tattaunawarsa da Aminiya ya ce ida har mawaki yana da abin da zai fada to mutane za su saurari wakokinsa kuma hakan zai sa ya bunkasa: Mene ne tarihin rayuwarka? Marlo King: An haife […]
Umar Abubakar Umar wanda aka fi sani da Marlo-King sanannen mawakin Hip-Hop ne da ke tashe a Jihar Kano. A tattaunawarsa da Aminiya ya ce ida har mawaki yana da abin da zai fada to mutane za su saurari wakokinsa kuma hakan zai sa ya bunkasa:
Mene ne tarihin rayuwarka?
Marlo King: An haife ni a Gombe. A can na yi karatun firamare da sakandare. Bayan na kammala sai na tafi Makarantar Koyon Harkokin Kasuwanci da ke Kaduna inda na karanci harkar banki. Na fara aikin banki a Skye Bank. Bayan na bar aiki banki sai na mayar da hankalina kan harkar nishadantarwa. Dalilin haka ya sa na dawo Jihar Kano da zama. Ni dama can ina da sha’awar harkar fim. A yanzu haka na fara shiga harkokin fim gadan-gadan, domin bayan taka rawa a cikin fim ina so in kasance mai shiryawa kuma mai bayar da umarni. Kai a yanzu haka na fara rubuta labaran fim. A kwanan nan mun yi magana da Ali Nuhu har na fada masa cewa zan yi farin ciki idan zan kasance a cikin ayarinsa.
Yaushe ka fara waka kuma zuwa yanzu wakoki nawa ka yi?
Marlo King: Zan iya cewa tun ina karami na fara waka. Waka a jinina take. Ni ba zan iya rayuwa ba waka ba. A kowane hali nake idan ban yi waka ba, ba na jin dadi. Ina yin waka da Hausa da Ingilishi da Fulatanci da Farasanci. Ina sakin wakokina a shafukana na sada zumunta.
Ina da sutudiyo nawa na kaina. Kuma ina da kamfanina da matasa ke yin waka da diramar nishadantarwa mai suna Arewa Pocket. Alhamdulillahi muna samun alheri a wannan bangare. A yanzu haka da dan abin da nake samu daga waka nake kula da gidan marayuna mai suna Muna da Baki Orphanage Foundation a Unguwar Hotoro. Muna da marayu kimanin 20 wadanda muke yi musu komai na rayuwa. Koda yake na fara gudanar da gidan marayun ne daga dan abin da na samu a lokacin da nake aikin banki.
Na yi wakoki da dama da suka hada da Wonderful Mama da Kano Is My City da Ina neman Marlo Kueen da sauransu. Sai dai zan iya cewa a duk wakokin da na yi na fi son Wonderful Mama.
Yawanci ni idan zan yi waka ba na rubutawa, idan na saurari kida ne sai in yi waka daidai da kidan.
Ban taba yin albam ba sai a yanzu da na fara aiki a kan wani albam dina mai suna Arewa Pocket
Yaya kake ganin wakokin Hausa Hip-Hop a yanzu?
Marlo King: Alhamdulillah! A yanzu wakokin Hip-Hop suna samun karbuwa a wajen jama’a. A da ne ake zaginsu, amma a yanzu kusan kowane gida akwai mawaki misali idan ba waka yake ba to yana son waka.
Nan gaba ina kallon waka za ta zama hanyar samun kudi kamar dai yadda a yanzu ake samu a harkar kwallon kafa da kuma siyasa. Idan har mawaka suka tsaya suka yi abin da ya kamata.
Idan kika ga mawaki ba ya ci gaba, to ba shi da abin fadi. Amma in dai mawaki zai yi to za a saurare shi kuma zai bunkasa.
Dole mawaki idan zai yi waka ya zama yana kula da kalaman da zai yi amfani da su. Ya kuma duba al’adun mutanensa don ya yi daidai da abin da zai yi waka a kai.
Mawaka za su ci gaba idan har suka tsaya suka yi abin da ya kamata. Mawaki zai yi kokari ya yi koyi da wani mawaki da yake gabansa. Kamar ni akwai wani mawaki Boner Muhammad shi ne gwanina a harkar waka. Kuma a gaskiya ina kwaikwayon wakokinsa. Koda yake sai nan gaba zan fito da yanayin wakokinsa a wakokina.
Idan har mawaka muna so gwamnati ta tallafa mana to dole sai mun zama masu kirkira tare da taimakon kanmu. Wannan kuwa ya hada har da salon wakokinmu da kuma jigogin wakokinmu. Idan gwamnati ta ga da gaske mutum yake abu ne mai sauki ta taimaka masa. Misali mawaki zai duba abubuwan da ke damun al’umma wadanda gwamnati take kokari wajen ganin an yi maganin abin kamar batun shan miyagun kwayoyi da ke damun al’umma. Idan mutum ya dauki wannan fanni a wakarsa, na tabbata hukumomin da ke da alhaki a wannan bangare za su shigo ciki.
Kin ga a sheakrun baya Jihar Kaduna ta shirya Music Festibal wanda ta taimaka wa mawaka da tallafi. Mawaka da yawa sun amfana.
Wane sako kake da shi ga masoyanka?
Marlo King: Ina yi wa masoyana fatar alheri. Ba abin da zan ce da su sai godiya musamman game da soyayyar da suke yi min domin hakan shi ne yake ba ni kwarin gwiwa. Idan har masoyina zai yi min magana ta daya daga shafukana na sada zumunta to zan sanya sunansa a cikin sabuwar wakata da zan yi nan ba da dadewa ba. Kuma ina yi musu albishir cewa akwai albam dina da zai fito nan ba da jimawa ba.