Mawakan Kannywood mata da ba a san su ba
Mawakan Kannywood mata da aka san muryoyinsu amma ba a san su ba sosai.
Idan ana batun mawakan Hausa, musamman na Masana’antar Kannywood, a lokuta da dama an fi yin maganar mawaka mazan kawai, inda ake mantawa da matan duk kuwa da cewa suna taka rawa a wakokin.
A zamanin da, an yi fitattun mawaka mata a Arewa, irinsu Barmani Choge da Magajiya Dambatta da Uwaliya Mai Amada da sauransu, inda a wancan lokacin, duk da an fi sauraron mazan, matan ma sukan yi gogayya ne da su a fagen wakoki da nishadantarwa.
Kare ya kashe yaro dan shekara 10 a Ingila
Muhimman abubuwa 8 da suka faru a Kannywood cikin makon jiya
A wannan zamanin da ake ciki, kusan za a iya cewa an fi sanin murya da fuskar mawakiya Fati Labaran, wadda aka fi sani da Fati Nijar.
Wannan ne ya sa Aminiya ta zakulo fitattun mawaka mata na wannan zamanin da aka san muryoyinsu, amma ba a san su ba sosai.
Zuwaira Ismail
Zuwaira Ismail tsohuwar mawakiya ce a Masana’antar Kannywood da ta dade tana janzarenta.
Ta yi wakoki da dama a cikin kusan shekara 20 da ta yi tana rera wakokin Hausa.
Daga cikin wakokin da ta yi akwai wakar ‘Dawaiya’ da ‘Zagadada’ wadda ake cewa ‘Zagadada mai gida na kaina’ da ‘Ina sonka’ wadda ake cewa ‘Ina sonka, na yaba da halinka, kyan jiki da surarka, sahibi da hannunka ka ban ruwa’ da Sai watarana da sauransu.
Maryam Fantimoti
Maryam Fantimoti ana mata lakabi da ‘Maman Mawaka’ ita ma tsohuwar mawakiya ce. Daga cikin fitattun wakokinta akwai ‘Fantimoti’ da ‘Jigida’ wadda take cewa ‘Maza jigida mata jigida, batun nan ni ban gane ba’ da ‘Uwar gida, ran gida’.
Maryam Sangandali
Maryam A. Baba, wadda aka fi sani da Sangandali za a iya cewa an fi sanin fuskarta. Ita ma ta dade tana jan zarenta.
Daga cikin wakokinta fitattu akwai, ‘Sangadale’ da ‘Ki yi shiru Maryam A. Baba’, wadda take cewa a ciki, “Ki yi shiru Maryam A. Baba dauki hali, halin madalla.’
Ko a kwanakin nan ma ta yi wakoki na siyasa da sauransu, ciki har da wakar Abba Gida Gida da sauransu.
Jamila Sadi
Jamila tsohuwar matar fitaccen mawaki Sadi Sidi Sharifai ce.
Daga cikin fitattun wakokinta akwai, ‘Sarmadan’ wadda take cewa a ciki ‘Sarmadan, ya masoyi, samardan. Samardan har abada ni da kai babu rabewa’ da ‘Basaja’ da sauransu.
Shamsiyya Sadi
Shamsiyya Sadi ta dade tana wakoki har zuwa wannan lokaci kuma ita ma rainon Sadi Sidi Sharifai ce.
Daga cikin fitattun wakokinta akwai, ‘Da kai za mu karshen rayuwa’ da ‘Na yi sa’a’ da ta yi da Hamisu Breaker, wadda a ciki a cewa, ‘Na yi sa’ar diyar da ba ta jayayya’ da ‘Mutu ka raba’ da ta yi tare da Isah Ayagi da sauransu.
Hairat Abdullahi
Hairat za a iya cewa a yanzu ne take jan zarenta a masana’antar. Daga cikin wakokinta akwai, ‘Rariya’ da ‘Abin da yake raina’ da ‘Mansoor’ da ‘Ciwon Idanu’ da sauransu.
Akwai kuma mawaka irinsu Marigayiya Rabi Mustafa, wadda ta yi wakoki irinsu ‘Mudajala da ‘Badali da sauransu.
Rabi Mustapha ta rasu ne a watan Fabrailun shekarar 2014 a Kano.
Akwai kuma su Naja Ta Annabi da Sulaihat Sister da Fati Kawo da sauransu.