Mawakan siyasa da suka yi nadamar yi wa Buhari waka
Buhari ya gurgunta dukkan hukumomin gwamnati, dole sai an farfado da su.
A makon jiya ne fitaccen mawakin siyasa, wanda ya fi fice da wakokin tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, Dauda Kahutu Rarara ya yi wani taron manema labarai, inda a ciki ya caccaki Buhari cewa ya yi, “damalmama kasa kafin ya mika mulki” ga Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu.
Mawakin ya nuna cewa ya yi nadamar goyon bayan Buhari a baya, inda ya ce ya yi da-na-sanin yin haka.
A cewarsa, “Na yi nadamar goyon bayan Buhari, saboda na yi zaton zai gyara Nijeriya, amma hakan ba ta samu ba.
- An yi garkuwa da matan shugaban karamar hukuma a Jigawa
- Ana zargin mai unguwa da fyade da sa wa yarinya cutar HIV a Jigawa
“Buhari ya gurgunta dukkan hukumomin gwamnati, dole sai an farfado da su.”
A wani bangaren da ya fi tayar da kura, mawakin ya bayyana watan ukun farko na Shugaba Tinubu da wadanda suka yi shekara takwas na Buhari.
Ya ce ya sha kai karar Buhari wajen Masari, amma sai tsohon gwamnan ya rika cewa ya yi hakuri, inda ya kara da cewa yanzun ma da a ce ya sanar da niyyarsa ta fitowa ya yi jawabin, da ba za a bari ba.
Sai dai kuma da ya juya kan batun gwamnatin na yanzu, mawakin ya bayyana cewa ya bayar da gudunmuwa mai yawan gaske, inda a cewarsa ko a batun nadin ministoci a gwamnatin, kamata ya yi a ce an nemi shawararsa kafin a nada su.
Rarara ya ce akalla idan ma ba a ba shi kujerar mukami ba, to kamata ya yi a ce an yi shawara da shi wajen nada su.
Ya kuma yi zargin cewa an nada makiyan Tinubu da dama mukamai a cikin kunshin gwamnatinsa.
Rarara ya kuma bugi kirjin cewa a duk fadin Arewacin Najeriya, idan ban da tsohon Gwamnan Kano, Dokta Abdulahi Umar Ganduje da na Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari, babu wanda ya ba tafiyar Tinubu gudunmawa kamar sa.
Sai dai ya ce babu wasu kudi da ya amfana da su a gwamnatin Buhari, inda ya kalubalanci masu ikirarin ya samu su kawo hujjar hakan.
Lamarin Rarara akwai rashin hankali da butulci — Bashir Ahmed
To sai dai bullar kalaman ke da wuya, wasu hadiman tsohon Shugaban, irin su mai taimaka masa kan harkokin kafafen sada zumunta na zamani, Bashir Ahmad, suka shiga yi masa luguden martani.
A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook da yammacin Alhamis din makon jiya, Bashir ya kwatanta kalaman na Rarara da butulci ga tsohon ubangidan nasa, inda ya ce duk wata daukaka da mawakin ya samu, sanadiyyar alakarsa da Buhari ce.
Ya ce “Na kalli wani bangare na bidiyon da yake yawo na taron manema labarai da mawaki Dauda Kahutu Rarara ya gabatar, musamman bangarorin da ya ci wa tsohon Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari mutunci tare da zargin cewa sai da ya rusa kasar baki daya kafin ya bar mulki.
“Bayan kammala kallon bidiyon na yi yunkurin ba wa Rarara amsa daya bayan daya ga duk wadannan zarge-zargen da ya yi, sai dai daga bisani da na sake yin nazari a tsanake sai na ga babu bukatar hakan a hankance da kuma mutunce, saboda wasu dalilai kwarara guda biyu.
“Na farko, cikin bidiyon, Rarara ya yi ikirarin cewa wai gudunmawar da ya bayar a tafiyar Buhari ko shi Buharin bai ba wa kan sa irin wannnan gudunmawa ba. Ikon Allah. Don Allah akwai hankali a cikin wannan magana?
“Sai dalili na biyu, inda yake cewa a wannan gwamnatin ta Shugaba Tinubu idan har ba a ba shi mukamin minista ba, to ya kamata a ce an kira shi an zauna da shi an zabi wadanda za a ba wa mukaman na ministoci. Tashin hankali.
“To gaskiya wanda maganganu da suka fita daga bakin mawakin ya sa na ga cewa tsayawa a ba shi amsa a matakin hankali ma bata lokaci ne.
“Domin kuwa wadannan maganganun na sa sun saba da kowane irin hankali da tunani, idan dai ba akwai rashin lafiya ba, to lalle akwai tsantsar jahilci. Babu hikima a cikin maganganun nasa ko kadan.
“Game da wakokin da ya yi wa Baba Buhari, tunda Rarara yake yi masa waka, bai taba yi masa waka kyauta ba tare da an biya shi hakkinsa ba,” kamar yadda Bashir ya wallafa.
Ba Rarara ya fara da-nasanin yi wa Buhari waka ba
Idan ba a manta ba, akwai mawakin siyasa Haruna Aliyu Ningi, wanda ya yi wakar “Shegiyar uwa mai kashe ’ya’yanta PDP’ shi ma ya taba yin da-na-sanin yi wa Buhari waka tun yana kan mulki.
A lokacin Haruna Ningi ya bayyana a wani faifan bidiyo cewa, “Na yi nadamar yi wa Buhari waka saboda bai cika alkawuran da ya dauka wa ’yan Nijeriya ba a lokacin da yake yakin neman zabe.”
Haka kuma akwai fitaccen mawaki, wanda shi ne ake wa lakabi da ‘Mai bakandamiyar Buhari’ Malam Ibrahim Yala, wanda ya yi wakar, “Yau Nijeriya riko sai Mai gaskiya, Baba Buhari kai muke so Nijeriya.”
A wata tattaunawarsa da Aminiya, Malam Yala ya ce shi ya saka wa Buhari sunan mai gaskiya.
A lokacin ne ya bayyana wa Aminiya cewa shi dai ya yi nadanar wakokin da ya yi wa Buhari, sannan ya nemi afuwar ’yan Nijeriya a lokacin.