Mawaki Abdu Wazirin dan Duna ya rasu
A ranar Talatar da ta gabata ne Allah Ya yi wa shahararren mawakin Hausa, Alhaji Abdu Wazirin danduna rasuwa.An yi jana’izar marigayin shekaranjiya Laraba. Ya rasu a asibitin Nassarawa da ke birnin Kano, inda aka kwantar da shi a sakamakon ciwon cikin da ya dade yana damunsa. dan marigayin Muhammad Sagir ya ce: “Har ma […]

A ranar Talatar da ta gabata ne Allah Ya yi wa shahararren mawakin Hausa, Alhaji Abdu Wazirin danduna rasuwa.
An yi jana’izar marigayin shekaranjiya Laraba.
Ya rasu a asibitin Nassarawa da ke birnin Kano, inda aka kwantar da shi a sakamakon ciwon cikin da ya dade yana damunsa.
dan marigayin Muhammad Sagir ya ce: “Har ma ana shirin yi masa tiyata, sai Allah Ya yi masa rasuwa.”
Ya mutu yana da shekara 86 a duniya, ya bar mata biyu Hasiya da A’isha da ‘ya’ya takwas , maza hudu, mata hudu.
Marigayin dan asalin garin Yaryasa ne da ke karamar Hukumar Tudun Wadan dankadai a Jihar Kano, daga baya ya koma unguwar Sheka da ke cikin Kano da zama har zuwa mutuwarsa.
Marigayin dan gidan malamai ne, ya kuma hardace kur’ani.
A cikin wakokinsa akwai ‘Sarkin karaye Abubakar’ da ‘Duniya Da Wuyar Zama’ da ‘Tsakanin dan Adam da Kudi’ da kuma bakandamiyarsa wakar marigayi ‘Sarkin Kano Sunusi’.