Mawaki Abubakar Ladan ya rasu

A ranar Talata ce Allah Ya yi wa shahararren mawakin Hausa Dokta Abubakar Ladan Zariya rasuwa. Ya rasu ne da misalin karfe 11 na dare. Marigayin ya yi gwagwarmayar fadakar da al’umma ta hanyar wakokin Hausa. Ya yi kokari wajen wayar da kan al’umma kan batutuwan da suka shafi siyasa da tarihi da kuma zamantakewa. […]

Mawaki Abubakar Ladan ya rasu

A ranar Talata ce Allah Ya yi wa shahararren mawakin Hausa Dokta Abubakar Ladan Zariya rasuwa.
Ya rasu ne da misalin karfe 11 na dare. Marigayin ya yi gwagwarmayar fadakar da al’umma ta hanyar wakokin Hausa. Ya yi kokari wajen wayar da kan al’umma kan batutuwan da suka shafi siyasa da tarihi da kuma zamantakewa. Ya yi yaki wajen hana kangin bauta a kasashenmu na Afirka. Ya yi wakokin a kan yadda Turawa suka gudanar da mulkin mallaka a kasashen Afirka.
An yi jana’izar marigayin a ranar Laraba da misalin 10 na safe a gidansa da ke Unguwar Kwarbai a cikin birnin Zariya na Jihar Kaduna.
Aminiya ta zanta da kanin marigayi mai suna Ahmad Maccido wanda suke unguwa daya, inda ya bayar da tarihin marigayin.
Ya ce, “Mun taso tare da marigayi Abubakar Ladan kamar shekara 78 da ta gabata.  Da farko ya yi makarantar Town School, daga nan ya je makarantar Midil, yana gaf da gamawa sai ya koma Kano, ya zauna na dan wani lokaci, inda ya yi aikin kamfani na dan kankanen lokaci. Daga nan ya dawo gida, bayan wani lokaci sai ya sake fita, bai dawo ba sai bayan shekara fiye da 10. A lokacin hankalinmu ya tashi, daga baya muka samu labarin yana wata kasa a Afirka. Bayan ya dawo gida ne ya yi mini bayanin ya zagaye kasashen Afirka gaba daya.”
Ya ce marigayin ya fada masa ya zagaye kasashen ne don ya yi wakoki domin hada kan Afirka gada daya, inda tun daga wannan lokacin ne ya fara tattara bayanai a kan kasashen Afirka da kuma tunanin yadda zai rera wakokin.
“Haka ya rika fama har ya rera su. Wannan shi ne abin da zan iya tunawa dangane da dalilin da ya sa ya zagaye kasashen Afirka. A lokacin da yake makaranta yana daya daga cikin daliban da suka iya wasan kwaikwayo. A lokacin yana Alhudahuda aka shirya wasan kwaikwayo, a wancan lokacin shi ne ya yi wakar Shata da har irin dabi’un da Shata yake yi ya rika yi, har ana kiransa Shatan Zariya, to wadansu daga cikin abubuwan da na sani ke nan a lokacin da yake makaranta.
“Idan ya samu hutu tare muke yawo, domin a lokacin ina karami, idan hutu ya kare da kyar muke rabuwa. Marigayi mutum ne mai jama’a, domin na san lokacin da ya gama zagaye kasashen Afirka ya dawo nan gida, akwai lokacin da aka yi zaben kai-da-halinka a wancan lokacin, ba a karkashin jam’iyyu ake yi ba, to a wannan ni na matsa masa ya tsaya takara a yankin Unguwar Kwarbai, a  lokacin ana kiran ta Unguwar Datti, to ya tsaya takarar, kuma ya ci zabe, to da yake zaben hawa-hawa ne, to a hawa na biyu ne ya janye saboda an zaunar da su, an hada kawunansu aka nemi wadansu su janye su bar wa wadansu, to tun a wannan lokacin ya nuna shi na jama’a ne.” Inji Maccido
Ya ce, kamar kwana biyar da ta wuce Farfesa Ango Abdullahi ya kawo musu ziyara, inda suka yi lissafin shekaru, inda Farfesa ya ce ya kai shekara 80, a nan suka gane marigayi ya girme shi da shekara 2. “Ka ga akalla yanzu shekarunsa sun kai 82 ke nan, wannan ina nufin a shekarar Musulunci ke nan.” Inji shi.
Uwargidar marigayi Bilkisu Sa’adu ta ce shekararsu fiye da 30 da aure, sannan ’ya’yansu 9,
“Ya’yansa 11 ne, amma muna da ’ya’ya 9 tsakanina da shi. Yana da jikoki 11. Mun yi zaman lafiya da marigayin, ya aure ni tun ina ’yar shekara 18. Ban taba yaji ba. Ya rike ni da amana. Allah Ya gafarta masa.” Ta ce cikin kuka.
daya daga cikin daliban marigayin Ambasada Sule Buba wanda da shi aka yi jana’izar marigayin, ya ce marigayin malaminsa ne a fannin siyasa. “Marigayi masani ne a fannin siyasar duniya, yana da jajircewa wajen ganin an tabbatar da ’yancin dan Adam. Ya ba ni shawarwari dangane da abubuwan da suka shafi siyasa.” Inji shi.
Babban dan marigayi namiji, Aliyu Abubakar Ladan Zariya, ya ce mahaifinsu ya ja shi a jika, ya mayar da shi tamkar abokinsa.
Ya ce, “Mahaifinmu ya yi mana riko irin wanda ba za mu taba mantawa da shi ba, domin mu goma 11 ne, haka ya ba mu ingantacciyar tarbiyya, don haka muna rokon Allah Ya gafarta masa. Mahaifina ya janyo ni kusa da shi tamkar abokinsa, domin idan ka ga yadda muke zaune tare za ka dauka mu abokai ne, musamman ma idan ba ka san mu ba, kuma cikin irin gudunmawar da mahaifinmu ya bayar wajen wayar da kan al’ummar Afirka, ya samu lambar yabo masu yawa.”
Ya ce a cikin lambobin yabon da aka ba shi akwai wacce “ni ne na wakilce shi, ni na karbo masa, kuma ita ce ta karshe, wato a ranar 29 ga Satumba, 2014 ke nan. Lambar yabon ita ce wacce Shugaban kasa ya ba shi; an ba shi lambar yabo ne ta OON ne, an kuma ba shi ita ce sakamakon irin gudunmuwar da ya ba Najeriya da Afirka da kuma duniya gaba daya. Mun gode wa wadanda suka taimaka mana.”
Dubban jama’a ne suka halarci jana’izar marigayin, inda daga cikinsu akwai mai sharhi a kan al’amuran yau da kullum, kuma shahararren marubuci Dokta Aliya Tilde.
Marigayin ya rasu yana da shekara 82, ya bar mata daya da ’ya’ya goma 11; maza 6, mata 5 da kuma jikoki 11.

Tinubu ya dawo Abuja bayan halartar taro a Saudiyya

Zaɓen Ondo: Atiku ya gargaɗi INEC kan tafka maguɗin zaɓe

Sojoji sun tafka ƙazamin artabu da Bello Turji a Sakkwato 

Mutum 10 sun rasu a hatsarin mota a Jigawa