Mawaki Eddie bedder ya kwankwashi kan Isra’ila a dandali
Eddie bedder mawaki ne dan Amurka. A Juma’ar da ta gabata ce ya gabatar wasa a Milton Keynes da ke Ingila, inda a dandalin ne ya yi amfani da wannnan dama ya la’anci kasar Isra’ila ta yin amfani da shagube.Wadanda suka kalli wasan ko kuma suka saurari wakar ta akwatunan talabijin ko ta fasahar Youtube […]

Eddie bedder mawaki ne dan Amurka. A Juma’ar da ta gabata ce ya gabatar wasa a Milton Keynes da ke Ingila, inda a dandalin ne ya yi amfani da wannnan dama ya la’anci kasar Isra’ila ta yin amfani da shagube.
Wadanda suka kalli wasan ko kuma suka saurari wakar ta akwatunan talabijin ko ta fasahar Youtube sun jiwo mawakin yana surfa wa Isra’ila zagi, tare da la’antarta, wanda haka ya nuna cewa yana adawa da hare-haren rokoki da kasar ke kai wa Palasdinu, inda sanadiyyar haka rayuka sama da dari biyu suka salwanta.
A wata waka da suka gabatar mai taken No More War (Babu Sauran Yaki), bedder ya juyo wajen dinbin ’yan kallo yana cewa: “Allah wadarai, Allah wadarai! Za mu iya samun yanayin da al’umma za su kasance cikin wadata, al’umma masu kawo zaman lafiya, mu kasance cikin lokaci na zaman lafiya. Za mu iya samun na’urorin da aka samar na zamani, yadda za mu iya musabaha da abokanmu…Kuma a daidai lokacin nan ne abin takaici ke faruwa, ba ma can da nisa ba, inda mutane ke ta luguden bama-bamai ga juna.”
A wani wurin kuma, mawakin ya ci gaba da yi wa Isra’ila shagube, yake cewa: “Idan da yakin ya zama dole, zan iya ganewa. Da abokan adawarku ne suka tsokane ku, zan iya ganewa. Na san kam ba za ku buraci shiga wannan yanayi ba. Amma na rantse da Allah, akwai wasu mutane a cikinku, da ke neman sanadin da za su yi kisa.”
Daga karshe, mawakin ya nuna fushinsa sosai kan Yahudawan na Isra’ila, inda ya rika cewa: Suna neman dalili ne kawai, domin su tsallaka makwabtansu, su kwaci kasar da ba tasu ba. Lallai ne su fita daga kasar nan, lallai ne su shiga taitayinsu, su daina kashe bayin Allah haka nan, yanzu-yanzu! Ba mu son mu ba su kudinmu, ba za mu amince su amshi harajinmu ba, domin su jefa wa yara bama-bamai.”
Haka kuma ya karkare wakar tasa da yin nasiha ga al’umma, yana cewa shi bai ga amfanin yaki ba. “Ku ci abinci, ku hayayyafa, ku samu nishadi daga ayyukan fasaha, ku saurari wakoki…ku ci abinci, ku yi aiki, ku yi soyayya, soyayya, soyayya, shin ina dalilin yaki?
Tuni dai Yahudawan da suka karanta bayanin nasa a kafafen sada zumunta na intanet suka yi ta yin Allah wadai da wakar tasa.