Mawaki Hassan Wayam ya riga mu gidan gaskiya

A cikin shekarar 1956 aka haifi Alhaji Hassan Wayam a wani gari mai suna Gwadda.

Mawaki Hassan Wayam ya riga mu gidan gaskiya

Hassan Wayam

Allah ya yiwa shahararran mawakin nan na Hausa, Alhaji Hassan Wayam mai wakar Kukuma Easy rasuwa a cikin daren jiya.

An yi jana’izarsa yau Asabar da misalin karfe 9:00 na safe a gigansa da ke layin Zomo a Unguwar Falladan da ke Karamar Hukumar Sabon Gari a Zariya.

Tarihi ya nuna cewa a cikin shekarar 1956 aka haifi Alhaji Hassan Wayam a wani gari mai suna Gwadda, wanda kuma ake kira Bakin Ruba, a kasar Maradun ta Jihar Zamfara.

Mahaifin sa, Malam Muhammadu Babarbare ne mai sana’ar sassaka yayin da a wasu lokutan ya rika yi wa Fulani kidan kotso jefi-jefi.

Bayan Hassan ya kara wayo, sai ya koma garin Mayanci da ke kusa da Gusau, ya zama yaron kanikawa.

Kasancewar Mayanci bariki ce sosai a wancan lokacin, ga karuwai da ‘yan caca da sauran ‘yan duniya, a nan ne sha’awar sa da kade-kade ta yi zurfi, musamman kidan kukuma.