Mawaki Mohammed Jammal ya ba da kyautar alluna ga makarantar da yake hidimar kasa

Shahararen mawaki Mohammed Jammal da ake wa lakabin Taka Rawa (White Nigerian) ya ba da  kyautar alluna ga makarantar da yake hidimar kasa.Mawakin ya sanya hotunansa a shafin facebook da kuma twitter a lokacin da yake mika kyaututtukan allunan ga makarantar sakandare ta St. Pauls and Debbies da ke Karu, Jihar Nassarawa.Mawakin na koyar da […]

Mawaki Mohammed Jammal ya ba da kyautar alluna ga makarantar da yake hidimar kasa
Mawaki Mohammed Jammal ya ba da kyautar alluna ga makarantar da yake hidimar kasa

Shahararen mawaki Mohammed Jammal da ake wa lakabin Taka Rawa (White Nigerian) ya ba da  kyautar alluna ga makarantar da yake hidimar kasa.
Mawakin ya sanya hotunansa a shafin facebook da kuma twitter a lokacin da yake mika kyaututtukan allunan ga makarantar sakandare ta St. Pauls and Debbies da ke Karu, Jihar Nassarawa.
Mawakin na koyar da kwamfyuta daga aji daya zuwa uku na karamar sakandaren.
Malamai da dalibai sun nuna farin cikinsu kan kyautar da mawakin ya yi musu.
“Mun yi farin ciki sakamakon kyautar da ya ba mu, kuma hakan zai taimaka wurin samar da ilimi mai inganci, kasancewar sai da kayan aiki ake samun ilimi mai inganci.” Inji Paul Musa, dan aji uku a makarantar.
Idan ba za a manta ba a ranar Lahadi 23 ga watan Yuni, 2013 yayin bikin barkwanci na AY Libe Show da aka yi a Thisday Dome a Abuja mawakin ya nemi budurwarsa ta yarda za ta aure shi.
Mawakin ya hau dandamalin dakin taron rike da zobe, sannan ya nufi wurin budurwarsa Maricel Romero, daga bisani ya durkusa a lokaci guda ya fara rokon ta yarda ta aure shi, bayan allon majigin ya rubuta ‘will you marry me?’ (shin za ki aure ni?). Daga nan ya ci gaba da rokonta. Bayan ta amince ne ya sanya mata zobe, sannan jama’a suka fara tafi.