Mawakin Indiya Bappi Lahiri ya cika shekara 61 a duniya

A Larabar da ta gabata ce shahararren mawakin fina-finan Indiya, Bappi Lahiri ya cika shekaru 61 a duniya. Tun kafin zuwan ranar, ’yan uwa da abokan arziki suka rika taya shi murna, a yayin da kuma suka shirya gagarumin biki domin taya shi murna.Mawakin dai an haife shi ne a ranar 27 ga watan Nuwamba, […]

Mawakin Indiya Bappi Lahiri ya cika shekara 61 a duniya

????????????????????????????????????

A Larabar da ta gabata ce shahararren mawakin fina-finan Indiya, Bappi Lahiri ya cika shekaru 61 a duniya. Tun kafin zuwan ranar, ’yan uwa da abokan arziki suka rika taya shi murna, a yayin da kuma suka shirya gagarumin biki domin taya shi murna.
Mawakin dai an haife shi ne a ranar 27 ga watan Nuwamba, 1952. Ya kasance daya daga cikin fitattun mawakan fina-finan Indiya, inda daga bisani ma ya zama daraktan wakokin, inda shi ke bayar da umurni wajen dauka ko shirya wakokin fina-finan. Kamar yadda bayani ya tabbata, shi ne mawaki na farko da ya fara gabatar da wakar zamani, mai dauke da kidan disko a fina-finan Indiya.
Bappi Mai Sarkar Gwal, kamar yadda ake masa lakabi, ya shahara sosai a shekarun 1980 da 1990, inda wakokin fina-finan ‘Disco Dancer’ da ‘Namak Halal’ da ‘Gang Leader’ da ‘Sharaabi’ suka daga martabarsa a cikin tsararrakinsa.
Tun da farko dai, Bappi ya koma birnin Mumbai da zama tun yana dan shekara 19 a duniya. Fim na farko da ya fara rera wa waka shi ne ‘Nahna Shikari,’ a 1973. Fim na farko da ya fara daga likkafarsa a harkar waka, shi ne fim din ‘Zakhme’ wanda Tahir Hussain ya shirya a 1975. Bappi ne ya shirya kidan wakokin fim din sannan kuma ya rera su da kansa. Ya hadu da mawaka biyu, Muhammad Rafi da Kishore Kumar, inda suka rera wakar ‘Nothing is Impossible’ a cikin fim din. A 1976 kuwa, wakokin fim din ‘Chalte-Chalte’ da ya rera sun zama fitattu, wadanda ake yayi.
Binciken Aminiya ya gano cewa, Bappi Lahiri ne ya kasance mawakin da ya iya shirya wakokin da suka dace da Mithun Chakraborty, wanda shi ne dan wasa na farko da ya kware wajen taka rawar disko a fina-finan Indiya. Sai da ta kai ga sunayen Bappi Lahiri da Mithun Chakraborty suka zama abin ambato, idan dai ana batun kida da wakar zamani a fina-finan Indiya, musamman a shekarun 1990.