Mawakin Shugaba Buhari, Malam Yala ya ajiye mukaminsa

Fitaccen dan siyasa, kuma mawakin siyasar nan da ya rera wakar ‘Yau Najeriya riko sai mai gaskiya,’ Malam Ibrahim Sale, wanda aka fi sani da Malam Yala ya ajiye mukaminsa. Yala, wanda shi ne Mai ba Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kaduna, Honourable Yusuf Ibrahim Zailani, shawara kan harkokin watsa labarai, ya bayyana hakan ne a […]

Mawakin Shugaba Buhari, Malam Yala ya ajiye mukaminsa

Fitaccen dan siyasa, kuma mawakin siyasar nan da ya rera wakar ‘Yau Najeriya riko sai mai gaskiya,’ Malam Ibrahim Sale, wanda aka fi sani da Malam Yala ya ajiye mukaminsa.

Yala, wanda shi ne Mai ba Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kaduna, Honourable Yusuf Ibrahim Zailani, shawara kan harkokin watsa labarai, ya bayyana hakan ne a shafinsa na Instagram a ranar Talata.

“A jiya 28 ga watan Satumba na 2020 na sauka daga kan mukamina na mai bai wa Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kaduna shawara kan harkokin watsa labarai.

“Ina mai amfani da wannan damar domin godiya ga Shugaban Majalisar saboda damar da ya ba ni na yin aiki a karkashinsa,” inji Yala.

Malam Yala dan siyasa ne a Kaduna, inda ya kasance Darakta Janar na Yakin Neman Zaben Sanata Uba Sani a zaben 2019.

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya