Mawakiya Janet Jackson ta dawo fage bayan boyon shekara daya
A makon jiya ne shahararriyar mawakiyar nan, Janet Jackson ta bayyana a gaban dandazon ’yan kallo, ta yi wasa, bayan shekara daya cur da rashin jin duriyar ta. Janet ’yar shekara 45, wacce kanwa ce ga shahararren mawakin nan marigayi Michael Jackson ta kwashe tsawon shekara daya ba tare da ta fito ta yi wasa […]
A makon jiya ne shahararriyar mawakiyar nan, Janet Jackson ta bayyana a gaban dandazon ’yan kallo, ta yi wasa, bayan shekara daya cur da rashin jin duriyar ta.
Janet ’yar shekara 45, wacce kanwa ce ga shahararren mawakin nan marigayi Michael Jackson ta kwashe tsawon shekara daya ba tare da ta fito ta yi wasa gaban mutane ba, a Juma’ar da ta gabata sai ga shi ta gabatar da wani kasaitaccen wasa a gidan rakashewa mai suna bogue Fashion Dubai a kasar Hadaddar Daular Larabawa.
Mawakiyar, wacce ta shahara da wakarta mai taken ‘Miss You Much’ ta yi wasanta na karshe ne a watan Mayu na bara a kasar Faransa, inda ta yi wasa domin gangamin nuna alhini game da cutar kanjamau. Tun daga lokacin ba a kara ganinta a bainar jama’a ba sai bana.
Janet dai ta bayyana ne gaban ’yan kallo dauke da wata kayatattar kwalliya ta musamman. Tana sanye da wata doguwar bakar rigar siliki mai dogon hannu. Hannayenta sun sha zanen kunshin zamani, irin na Indiyawa.