Mawakiya Kate Bush ta dawo waka bayan shekara 35: An sayi tikitin kallonta dubu 80 cikin minti 15
An sayar da tikitin shiga kallon wasa mawakiyar Amurka dubu 80 cikin minti 15. Wannan mawakiya ’yar shekara 56, wadda ta daina waka tun a shekarar 1979.Masoyan wannan mawakiya Kate Bush, sun yi murnar dawowarta, inda suka ce su ma ba za a bar su a baya ba, sai sun shiga kundin tarihi. Cincirindon ’yan […]
An sayar da tikitin shiga kallon wasa mawakiyar Amurka dubu 80 cikin minti 15. Wannan mawakiya ’yar shekara 56, wadda ta daina waka tun a shekarar 1979.
Masoyan wannan mawakiya Kate Bush, sun yi murnar dawowarta, inda suka ce su ma ba za a bar su a baya ba, sai sun shiga kundin tarihi. Cincirindon ’yan kallon sun yi ta dururuwa, don kallon wannan mawakiya sanye da bakar rika, sannan ta fara yin wakara “Lily.”
Wakokin da ta rera 11, sun kasance cikin jerin wakoki 100 da suke tashe, kuma ana ta cin kasuwarsu. Babbar kwakarta mai taken “The Whole Story – daukacin labara,” ita ta zamo waka ta takwas a jerin wakoki 100 da ke tashe a Amurka, kamar yadda shafin sadarwa na OfficialCharts.com ya ruwaito
Sannan wakarta mai taken “50 Words Of Snow” ita ma ta yi tashe, inda aka sayar da kofin faifanta guda dubu 155, kamar yadda kamfanin charts ya bayyana.
Da take rubutu a shafin sadarwarta, mawakiyar ta ce “ta cika da matukar mamakin,” game da irin tarbar da ta samu. Sai dai ta roki masoyanta da su ajiye kayan kallon wakarta a gida.