Mawakiya ’yar Amurka Jennifer Grout ta musulunta
A Lahadin da ta gabata ce matashiyar mawakiya ’yar Amurka, Jennifer Grout ta amshi Musulunci, kamar yadda wani faifan bidiyo na YouTube ya ruwaito.Mawakiyar, ’yar shekara 23 da haihuwa ta kware ne wajen rera wakokin fasaha na Larabawan dauri, duk kuwa da cewa ita ba Balarabiya ba ce kuma ba ta taba nazartar harshen Larabci […]

A Lahadin da ta gabata ce matashiyar mawakiya ’yar Amurka, Jennifer Grout ta amshi Musulunci, kamar yadda wani faifan bidiyo na YouTube ya ruwaito.
Mawakiyar, ’yar shekara 23 da haihuwa ta kware ne wajen rera wakokin fasaha na Larabawan dauri, duk kuwa da cewa ita ba Balarabiya ba ce kuma ba ta taba nazartar harshen Larabci ba.
A faifan bidiyon, an nuno mawakiya Jennifer a gaban wasu mutane biyu tana furta kalmar shahada: “La’ilaha illallah, Muhammadur rasulillah” (Babu wani abin bautawa sai Allah kuma Muhammadu manzonSa ne).
Kafar watsa labarai ta intanet da ke kasar Morocco, ‘Morocco World News’ ta tabbatar da ingancin labarin musuluntar mawakiyar, inda ta ce an dauki faifan bidiyon ne a birnin Fez, inda ita Jennifer take zaune a halin yanzu.
Kamar yadda binciken Aminiya ya tabbatar, mawakiyar tana zaune ne a kasar Morocco, inda take nazarin harshen Larabci. Wata majiya ta tabbatar da cewa daya daga cikin mutane biyu da ke tare da ita, a lokacin da take furta kalmar shahada, saurayinta ne, wanda ake kyautata zaton cewa shi zai aure ta.