Mayaƙan Boko Haram 263 sun miƙa wuya — MNJTF
Binciken farko ya gano cewa mutanen da suka miƙa wuyan ’yan Najeriya da Kamaru ne.
Aƙalla mayaƙan Boko Haram 263 da iyalansu ne suka miƙa wuya ga dakarun Rundunar Hadin Gwiwa ta Yankin Tafkin Chadi (MNJTF) a Kamaru.
Hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na MNJTF a birnin N’djamena na Chadi, Laftanal Kanal Abubakar Abdullahi ya fitar a ranar Juma’a.
- Pakistan ta kama Amin Ul-Haq wani na kusa da Osama Bin Laden
- ‘N70,000 a matsayin mafi karancin albashi ya yi kadan’
Rundunar ta ce binciken farko-farko ya nuna cewa mutanen ‘yan asalin garuruwan Tumbuma da Kutumgulla ne a ƙaramar hukumar Marte a Nijeriya.
Laftanal Kanal Abdullahi ya ƙara da cewa tun ranar 11 ga watan Yulin 2024 aka fara samun tururuwar ‘yan ta’addan da ke miƙa wuya ga rundunar a Wulgo da ke kan iyakar Nijeriya da Kamaru.
“A ranar ce kuma wani mutum mai suna Malam Kori Bukar mai shekara 50 ya tsere daga maɓoyarsu da ke Jibilaram ya miƙa wuya ga sojoji,” a cewar sanarwar.
“Sannan a ranar 11 ga watan Yuli sai wasu ‘yan ta’adda 19 suka miƙa wuya a ƙauyen Madaya da ke yankin Arewa mai nisa na Kamaru, sai kuma wasu 11 da suka miƙa wuya a Wulgo daga maɓoyarsu ta Tumbuma.
“A ranar 12 ga Yulin 2024 kuma mutum 64 sun miƙa wuya a Bonderi da ke Kamaru, da suka haɗa da maza manya shida da mata 20 da yara 38. ‘Yan ta’adda 27 sun sake miƙa wuya ranar 13 ga watan Yuli,” a cewar rundunar ta MNJTF.
An ci gaba da samun hakan a ranar 15 ga Yuli, 2024, inda wasu mutum 102 da suka miƙa wuya a Bonderi, yankin Arewa mai nisa na Kamaru, ciki har da manya maza 20, mata 40, da yara 42.
“Bugu da ƙari, wasu mutum biyar sun miƙa wuya a Wulgo, inda biyu suka fito daga maɓoyar Tumbuma da ke Kudancin Tafkin Chadi.
A ranar 16 ga Yuli 2024, wasu ’yan ta’adda biyu sun miƙa wuya. Sai washegari, 17 ga Yuli kuma an samu jimillar ’yan ta’adda 48 da iyalansu sun miƙa wuya, wadanda suka hada da manya maza 10, mata 15, da yara 23.
Binciken farko ya gano cewa mutanen da suka miƙa wuyan ’yan Najeriya da Kamaru ne, kamar yadda sanarwar ta yi ƙarin haske, tana mai cewa an miƙa ’yan Najeriyar a hannun sojojin rundunar Operation HADIN KAI, domin ɗaukar mataki na gaba.