Mayaƙan Boko Haram sun sace kwale-kwale 8 a Borno

A bayan nan dai mayaƙan Boko Haram na ci gaba da kafa sansani a gaɓar Tafkin Chadi musamman a yankunan Ƙaramar Hukumar Kukawa.

Mayaƙan Boko Haram sun sace kwale-kwale 8 a Borno

Wasu ’yan ta’adda da ake kyautata zaton mayaƙan Boko Haram ne sun yi fashi da makamin wasu kwale-kwalen kamun kifi guda takwas a hannun masunta a Doron Baga da ke Ƙaramar Hukumar Kukawa ta Jihar Borno.

Lamarin ya faru ne da yammacin ranar Asabar a ƙauyen Kaimo da ke da tazarar kilomita huɗu daga garin Doron Baga.

A cewar wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta, ‘yan ta’addan dauke da muggan makamai da ba a tabbatar da adadinsu ba, sun mamaye ƙauyen inda suka tara masuntan waje guda.

Majiyar ta ce “sun iso ne da makamai, inda suka yi barazanar tayar da hankali idan ba mu bar jiragen ruwanmu ba.”

Ya ƙara da cewa “daga nan ne ‘yan ta’addan suka ƙwace kwale-kwale guda takwas sannan suka tsere ta cikin kogin.

“Muna buƙatar gwamnati ta kawo mana agaji saboda sana’o’in da muke da su a halin yanzu su ne kamun kifi da noma, amma yanzu muna cikin firgici saboda daji ba shi da tsaro.”

A bayan nan dai rahotannin sun tabbatar da cewa ‘yan ta’addar Boko Haram na ci gaba da kafa sansani a gabar tafkin Chadi, musamman a Tumbun Alkali, Tumbun Barebari, Musarram, Shangaram, da Masharam, duk a cikin Ƙaramar Hukumar Kukawa ta Jihar Borno.