Mayaƙan Boko Haram sun sace mata 319 a Borno

Mun sha gargadin su a kan shiga daji ɗebo itacen girki a wuraren da mu tabbatar da amincin su ba.

Mayaƙan Boko Haram sun sace mata 319 a Borno

Rahotanni sun ce mayaƙan Boko Haram sun yi awon gaba da wasu mata 319 ‘yan gudun hijira a garin Ngala da ke Karamar Hukumar Gambarou Ngala ta Jihar Borno.

Wata majiya a sansanin gudun hijira na Babban Sansani ta ce mayaƙan na Boko Haram sun sace matan ne a lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa daji domin ɗebo itacen girki a ranar Lahadin da ta gabata.

Majiyar ta ce ’yan ta’addan sun yi wa matan ƙawanya ne a dajin Bula Kunte da ke Yammacin garin Ngala.

“Sun kyale tsofaffin da ke cikinsu sannan suka shiga daji da sauran ’yan mata 319 da kuma wasu samari.

“Amma, uku daga cikin ‘yan matan da suka tsere suka koma Ngala sun ce masu tayar da ƙayar bayan sun kai su wani daji kusa da ƙauyen Bukar-Mairam a Jamhuriyyar Chadi.

“Cikin duhun dare ’yan matan suka tsere bayan mayaƙan sun kwanta barci, inda suka shafe tsawon kwanaki biyu suna tafe a kasa kafin su isa Ngala.

“Yawancin ‘yan matan da lamarin ya rutsa da su sun fito ne daga sansanin Babban Sansani sauran kuma daga sansanin Zulum da Arab.

“Duk ’yan matan sun shiga jeji ne domin ɗebo itacen da suke sayarwa da kuma girkin abinci saboda wanda muke samu a sansanin ba ya wadatar da mu. Rayuwa tana da wahala a nan,” in ji shi.

Sai dai wata majiyar tsaro da ta tabbatar da faruwar lamarin, ta shaida wa Aminiya cewa, adadin matan da mayaƙan suka sace 113 ne.

“Labarin da muka samu shi ne cewa an sace mata 113 amma ba su kai 319 da ake ikirari ba.”

Kazalika, wata majiyar jami’an tsaron ta ce sun sha gargadin ‘yan gudun hijirar kan zuwa wasu yankuna a cikin daji saboda fargabar kai hari ko kuma faruwar irin hakan.

“A koda yaushe muna gargadin da su riƙa kai-komo a wurare masu aminci, amma matsin tattalin arziki ne ke sa akasarinsu shiga wasu wurare masu hatsari.

“Saboda ba su da wata hanyar dogara da kai da ta wuce ɗebo itacen a matsayin sana’a.

“A yanzu ana sayar da ƙaramin kwanon garin masara kan Naira 2,200, saboda haka a ina za su samu kuɗin siya.?

“Wannan yanayi da ake ci ya sanya ba za mu iya hana su neman abin dogaro da kai ba idan har mu ba za mu iya ciyar da su ba,” inji shi.

Aminiya ta ruwaito cewa, wannan dai na ɗaya daga cikin manya-manyan sace-sacen da aka yi a Borno, tun bayan sace ’yan mata 276 na Sakandaren Chibok da aka yi a ranar 14 ga watan Afrilun 2014.