Mayaƙan Lakurawa 3 sun shiga hannu kan bayar da cin hancin N1.6m

Rundunar ta jaddada aniyarta na ci gaba da yaƙi da aikata laifuka a jihar.

Mayaƙan Lakurawa 3 sun shiga hannu kan bayar da cin hancin N1.6m

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kebbi, ta kama wasu mayaƙan Lakurawa uku, yayin da suke ƙoƙarin bai wa jami’in da ke bincike a kansu, cin hancin Naira miliyan 1.6.

A cikin sanarwar da kakakin rundunar, SP Nafiu Abubakar, ya fitar, ya ce mutanen uku; Umaru Garba, Alhaji Abubakar Mamman, da Usman Muhammadu.

Mutanen sun yi ƙoƙarin bayar da cin hanci domin kawo tsaiko ga binciken da ake yi a kansu.

Sanarwar ta ce an kama waɗanda ake zargi nan take, kuma an fara bincike a kan lamarin.

Sanarwar ta ƙara da cewa, Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, Bello M. Sani, ya sake tabbatar da cewa rundunar za ta ci gaba da yaƙi da aikata laifuka.

Sannan ya jinjina wa jami’an rundunar kan yadda suka nuna gaskiya a lamarin, ta hanyar ƙin karɓar cin hancin da aka ba su.

Mutum 14 sun rasu sakamakon kamuwa da zazzabin Lassa a Taraba

’Yan bindiga sun harbi likita, sun sace mutum 5 a asibiti a Katsina

Manoma 7 sun rasu a hatsarin mota a Minna

Farashin litar mai zai haura N1,000 kwana nan — IPMAN