Mayakan Boko Haram sun mamaye al’ummomin Jihar Neja
An gano nakiyoyi da mayakan ne Boko Haram suka binne a yankin Shiroro.
Mayakan Boko Haram sun yi kakagida a wasu kananan hukumomi hudu a Jihar Neja inda suka tursasa wa mazauna yi musu biyayya da kuma saba wa hukumomin gwamnati.
Mazauna kauyuka a kananan hukumomin Shiroro, Rafi da Munya da Borgu na Jihar Neja na cikin zullumi game da abin da ke iya faruwa da su a nan gaba, saboda abin da suke ganin shi ne koluwar matsalar mahara a Jihar.
An kuma gano nakiyoyi da ake zargin mayakan na Boko Haram din ne suka binne a yankin Karamar Hukumar Shiroro ta Jihar.
Shugaban Karamar Hukumar Shiroro, Suleiman Chukuba, ya tabbatar da zargin da gwamnan jihar, Abubakar Sani-Bello, ya yi a ranar Lahadi cewa mayakan Boko Haram ne suka kai hari a Jihar ranar Lahadi.
A makonnin baya, mayakan da ake zargin ’yan Boko Haram ne sun kai wa kauyukan yankin Shiroro, Munya da Rafi hare-haren, inda suka hallaka mutane da dama.
Chukuba ya ce, “Game da shigowar Boko Haram Shiroro, akwai yankuna hudu da abin ya shafa,” kuma mazauna sun yi amannar ’yan Boko Haram ne saboda salonsu na wa’azi.
“Sun shaida wa mutane cewa suna da kudi da makamai da za su taimaka musu su yaki gwamnati, wanda shi ne akidar Boko Haram,” inji shi.
Ya ce sun samu bayani cewa mayakan na Boko Haram na tursasa wa mutane aurar da ’ya’yansu mata da suka kai shekara 12.
Ganau sun shaida mana cewa mayakan Boko Haram ne suka kawo musu harin, saboda salon hare-haren na irin na ’yan bindiga ba ne.
A cewarsu, masu mamayar sun umarce su da kar su sake su yi da’a ga kowace irin hukuma.
Shugaban Kungiyar Matasan Shiroro, Bello Ibrahim, ya ce maharan suna cin karensu ba babbaka.
“A lokaicin da suke kauyen Kawure, mahaifar tsohon sanata mai wakilatar Neja ta Gabas, David Umaru, rundunar sojojin hadin gwiwa sun watsa su amma daga baya sun sake dawowa saboda babu sansanin soji a yankin.
“Yanzu yanzu ba a iya kauyen Kawure suke ba akwai su a kauyen Kuregbe, Awulo da sauransu,” inda suke yin yadda suka ga dama.
“A kauyukan Awulo da Kuregbe ne suka tara mutane Musulmai da Kiristoci suka ba su umarni cewa duk yarinyar da ta kai shekar 12 a aurar da ita.”
Wasu mazauna yankunan sun tabbatar cewa mayakan na gudanar da harkokinsu ba tare da wata tangarda ba.
“Suna cudanya da mutanen kauyukan inda suka mayar da kansu hukuma, suna tursasa wa mutane yi musu biyayya.
“A Chukuba da Kuregbe, ’yan Boko Haram ne ba ’yan bindiga da aka sani ba,” inji su.
Wani mazaunin Shirori, Abubakar Sani Yusuf Kokki, ya ce yanayin shigar mayakan da ke wasu al’ummomin jihar ta tabbatar ’yan Boko Haram ne.
“A harin da suka kai kauyen Magami na Shiroro, sun shiga masallaci suna karatun Alkur’ani… Saboda haka salonsu ba irin na ’yan bindiga ba ne.”
Da yake tabbatar da mamayar, Darakta-Janar na Hukumar Agajin Gaggawa ta Jihar Neja (NSEMA), Ahmed Ibrahim Inga, ya ce harin ya sa an samu tururuwar mutanen da ke komawa sansannin ’yan gudun hijira a Jihar.
An dade ’yan bindiga na kai hare-hare suna kashe mutane su sace dabboki su kona gidaje gami da yi wa mata fyade a Jihar Neja da sauran jihohi kamar Zamfara, Katsina, Kaduna, Sakkwato da Kuma Kebbi.
A ranar Lahadi, Gwamann Abubakar Sani-Bello, wanda ya sha zargin cewa mayakan Boko Haram sun shiga jihar, ya nanata zargin nasa, wanda ya ce yana da nasaba da matsalar tsaro ta baya-bayan nan.
“Muna da hujjar da za mu ce wadannan ba ’yan bindgida ba ne, saboda sabon harin da suka kai ya nuna suna da tsari kuma sun samu horo,” inji shi.
Bayan wasu hare-hare da aka kai a kauyukan kananan hukumomin Shiroro da Munya gwamnan ya yi zargin cewa, “Ba ’yan bindiga ba ne, har da ’yan Boko Haram, wuri na gaba da suke son shiga shi ne Abuja, wanda daga nan bai fi tafiyar awa biyu ba a mota.”
Ya ce a kauyen Kaure da ke Karamar Hukumar Shiroro sun kafa tutar a Boko Haram kuma su ke iko da yankin.
A baya, kungiyoyin Ansarul-Islam da Darul-Salam sun yi dafifi a sassan jihar kafin daga bisani aka tarwatsa su.
Ganau sun shaida mana cewa mayakan Boko Haram ne suka kawo musu harin, saboda salon hare-haren na irin na ’yan bindiga ba ne.
A cewarsu, masu mamayar sun umarce su da kar su sake su yi da’a ga kowace irin hukuma.
Wasu mazauna yankunan sun tabbatar cewa mutanen na gudanar da harkokinsu ba tare da wata tangarda ba.
“Suna cudanya da mutanen kauyukan inda suka mayar da kansu hukuma, suna tursasa wa mutane yi musu biyayya.
“A Chukuba da Kuregbe, ’yan Boko Haram ne ba ’yan bindiga da aka sani ba,” inji shi.
Wani mazaunin Shirori, Abubakar Sani Yusuf Kokki, ya ce yanayin shigar mayakan da ke wasu al’ummomin jihar ta tabbatar ’yan Boko Haram ne.
“A harin da suka kai kauyen Magami na Shiroro, sun shiga masallaci suna karatun Alkur’ani… Saboda haka salonsu ba irin na ’yan bindiga ba ne.”
Aminiya ta kuma gano cewa mayakan sun yi sansani da Dajin Audu Fari da ke ke Karamar Hukumar Borgu ta jihar.
Wani mazaunin yankin ya ce mayakan sun dade da fara zama a cikin dajin.
Ganau sun shaida mana cewa mayakan Boko Haram ne suka kawo musu harin, saboda salon hare-haren na irin na ’yan bindiga ba ne.
A cewarsu, masu mamayar sun umarce su da kar su sake su yi da’a ga kowace irin hukuma.
Shugaban Kungiyar Matasan Shiroro, Bello Ibrahim, ya ce maharan suna cin karensu ba babbaka.
“A lokaicin da suke kauyen Kawure, mahaifar tsohon sanata mai wakilatar Neja ta Gabas, David Umaru, rundunar sojojin hadin gwiwa sun watsa su amma daga baya sun sake dawowa saboda babu sansanin soji a yankin.
“Yanzu yanzu ba a iya kauyen Kawure suke ba akwai su a kauyen Kuregbe, Awulo da sauransu,” inda suke yin yadda suka ga dama.
“A kauyukan Awulo da Kuregbe ne suka tara mutane Musulmai d Kiristaoci suka ba su umarni cewa duk yarinyar da ta kai shekar 12 a aurar da ita.”
Wasu mazauna yankunan sun tabbatar cewa mutanen na gudanar da harkokinsu ba tare da wata tangarda ba.
“Suna cudanya da mutanen kauyukan inda suka mayar da kansu hukuma, suna tursasa wa mutane yi musu biyayya.
“A Chukuba da Kuregbe, ’yan Boko Haram ne ba ’yan bindiga da aka sani ba,” inji shi.
Wani mazaunin Shirori, Abubakar Sani Yusuf Kokki, ya ce yanayin shigar mayakan da ke wasu al’ummomin jihar ta tabbatar ’yan Boko Haram ne.
“A harin da suka kai kauyen Magami na Shiroro, sun shiga masallaci suna karatun Alkur’ani… Saboda haka salonsu ba irin na ’yan bindiga ba ne.”
Wani mazaunin yankin Dajin Audu Fari da ke Karamar Hukumar Borgu ta jihar ya ce mayakan sun dade da fara zama a cikin dajin.
A wani sakon murya da mayakan suka aikwa Sarkin Audu Fari, an ji waninsu na cewa, “Mun shigo dajin nan ne saboda kai da iyayen gidanga, wato gwamnati ba kwa abin da ya dace. Muna kiran mutane zuwa ga Allah
“Turawa sun cusa muku al’adunsu, mu a wurinmu duk wanda ke bin gwamnati muna daukar sa ne a matsayin kafiri, ko da ya ce shi Musulumi ne,” inji mutumin.
A cewarsu, duk wani wanda ke hada baki da hukumomin tsaro ba za su raga masa ba, ko da dan banga ne.
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Neja da sojoji sun ke cewa uffan a kan lamarin.
Amma wani masanin harkar tasro ya ce ’yan Boko Haram mabiya Abubakar Shekau wanda ya kashe kansa ne suka mamaye yankin.
A cewarsa, tub bayan rasuwar Shekau mayakansa ke ta kmawa yankin Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya inda suke gudanar da ayyukansu tare da ’yan bindiga.
An dade ana ta kiran gwamnatin Najeriya da ta ayyana ’yan bindiga a matsayin ’yan ta’adda.
Daga: Abubakar Akote, Minna da Sagir Kano Saleh da Idowu Isamotu.