Mayakan ISIS na dab da kwace birnin Kobane na Siriya
Manzon musamman na Majalisar dunkin Duniya a kasar Siriya, Mista Staffan de Mistura, ya bukaci kasashen duniya su dauki dukkan matakan da suka wajaba domin baiwa Kurdawa mazauna birnin Kobane na kasar Syriya kariya daga mayakan ISIS da ke da’awar kafa Daular Musulunci a kasashen Iraki da SyriaKiran na Mistura na zuwa ne yayin da […]
Manzon musamman na Majalisar dunkin Duniya a kasar Siriya, Mista Staffan de Mistura, ya bukaci kasashen duniya su dauki dukkan matakan da suka wajaba domin baiwa Kurdawa mazauna birnin Kobane na kasar Syriya kariya daga mayakan ISIS da ke da’awar kafa Daular Musulunci a kasashen Iraki da Syria
Kiran na Mistura na zuwa ne yayin da rahotanni ke cewa tuni mayakan ISIS suka kutsa a cikin birnin na Kobane wanda ke daf da kan iyakar Siriya da Turkiyya.
Zuwa yanzu kasashe akalla 50 ne suka goyi bayan yakin da kasar Amurka ke yi da mayakan ISIS da suka lashi takobin far wa duk kasar da ta taimaka wa Amurka a fada musu da hari.
A bayan nan akwai wani zargi da ya fito daga Amurka cewa wasu kasashen Larabawa suna taimaka wa mayakan ISIS da kayan fada
Amma Mataimakin Shugaban Amurka, Sanata Joe Biden, ya nemi afuwa daga hukumomin kasar Saudiyya, bayan ya yi zargin cewa wasu daga cikin kasashen Larabawa cikinsu kuwa har da Saudiyya na taimaka wa mayakan ISIS da ke yankin.
Kafin nan Mataimakin Shugaban na Amurka ya nemi irin wannan afuwa daga kasashen Turkiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa wadanda suka nuna bacin ransu dangane da wannan zargi.