Mayakan ISIS sun kona littattafan tarihi 8000 a Mosul
A ranar Litinin da ta gabata ne mayakan ISIS suka kona littattafan tarihi da tsofaffin mukaloli da yawansu ya kai 8000 a dakin karatu da ke Mosul a kasar Iraki. “Mayakan ISIS sun kona dakin karatu da ke Mosul. Sun yi amfani da bam ne wajen kona dakin karatun. Mun roke su kada su kawo […]
A ranar Litinin da ta gabata ne mayakan ISIS suka kona littattafan tarihi da tsofaffin mukaloli da yawansu ya kai 8000 a dakin karatu da ke Mosul a kasar Iraki.
“Mayakan ISIS sun kona dakin karatu da ke Mosul. Sun yi amfani da bam ne wajen kona dakin karatun. Mun roke su kada su kawo wa dakin karatun hari amma suka ki saurararmu.” Inji Ghanim al-Ta’an, darakta na dakin karatun.
Tsohon mataimakin daraktan da ke kula da dakin karatun mai suna Faraj ya ce an bude dakin karatun ne a shekarar 1921. “A cikin abubuwan da aka yi asara bayan an kona dakin karatun sun hada da tsofaffin littattafai da mukaloli tun na karni na 18, da kuma littattafan da gidan dab’i na Syriac ya buga a karni na 19 da littattafan karnin Ottoman da jaridun Iraki a farkon karni na 20 da sauransu.
“A lokacin da Amurka ta kaddamar da yaki a kasar Iraki a shekarar 2003 wadansu bata-gari sun shiga dakin karatu inda suka sace abubuwa masu yawa, duk da cewa mutanen da suke kusa da dakin karatun sun adana wadansu muhimman abubuwan da aka ajiye a dakin karatun, inda daga baya wadansu masu kudi suka rika sayan kayayyakin da aka sace don inganta dakin karatun.” Inji Faraj.
“A wannan karon an kona littafin Aberroes da ya shekara 900. Mutane da yawa sun barke da kuka a lokacin da ake kona dakin karatun. Wannan abin takaici ne, nakan tuna a shekarar 1970 mukan je dakin karatun, inda aka rarraba littattafan bisa harrufa.” Inji Akil Kata, wani wanda ya yi gudun hijira daga Iraki zuwa Amurka.