Mayakan ISIS ‘sun yanke kan wani dan jarida’

Amurka ta ce tana kokarin tantance sahihancin wani hoton bidiyo, wanda ya nuna mayakan kungiyar ISIS suna datse kan wani dan jarida dan asalin kasar Amurkan mai suna James Foley.dan jaridan ya bace ne a Siriya, kimanin shekara biyu da suka wuce kuma tun lokacin ba a sake jin duriyarsa ba.Mahaifiyar marigayin, ta aike da […]

Mayakan ISIS ‘sun yanke kan wani dan jarida’
Mayakan ISIS ‘sun yanke kan wani dan jarida’

Amurka ta ce tana kokarin tantance sahihancin wani hoton bidiyo, wanda ya nuna mayakan kungiyar ISIS suna datse kan wani dan jarida dan asalin kasar Amurkan mai suna James Foley.
dan jaridan ya bace ne a Siriya, kimanin shekara biyu da suka wuce kuma tun lokacin ba a sake jin duriyarsa ba.
Mahaifiyar marigayin, ta aike da sakon juyayi ga dan nata, ta hanyar sadarwa ta Facebook, tana cewar ya rasa ransa ne a yayin da yake kokarin bayyana halin kunci da mutanen Siriya suka shiga.
Ta kuma yi kira ga wadanda suka sace shi, su ceci rayukan sauran mutanen da suke garkuwar da su. Ta bayyana cewar, ba su aikata laifin komai ba, kuma ba su da iko a kan manufar kasashen waje ta Amurka.
A ranar Talata ne kungiyar ta fitar da wani faifan bidiyo da ke bayyana yadda wani mayakinta ya datse kan Mista Foley. Kuma ta bai wa bidiyon sunan “Sako zuwa ga Amurka”, tana bayyana abun da aka aikata a ciki da wata ramuwar gayya ga farmakin da Amurkan ke kai wa mayakanta ta sama a kasar Iraki.
kungiyar tana da mayakan da suka zarce guda dubu 50 a Siriya kuma a watan da ya wuce ne wasu guda dubu shida suka samu horo a cewar wata kungiya da ke sanya idanu kan harkokin kungiyar.