Mayakan ISWAP jirgin soji ya kashe a Borno ba masunta ba

Hedikwatar Tsaro ta ce haramcin kamun kifi na na tana aiki.

Mayakan ISWAP jirgin soji ya kashe a Borno ba masunta ba

Jirgin yakin sojin saman Najeriya

Hedikwatar Tsaro ta Najeriya ta ce mayakan kungiyar ISWAP ne jiragen soji suka kashe a yankin Kwatan Daban Masara da ke Jihar Borno, ba masunta ba.

Hedikwatar ta bayyana cewa mayakan ISWAP ne suka yi shigar burtu a yankin Tabkin Chadi, inda suke kai hare-hare, amma jiragen sojin suka gano su, suka kuma yi luguden wuta a kan maboyar ’yan ta’addar.

Ta ce bayanin ya zama wajibi ne ganin yadda kafafen yada labarai ke ba da rahoto cewa fararen hula ne jiragen sojin suka kashe a bisa kuskure.

A sanarwar da ya fitar a daren Juma’a, kakakin Hedikwatar Tsaro, Birgediya Benard Onyeuko, ya ce mayakan na ISWAP din na boyewa a duhun jejin yankin Tabkin Chadin suna batar da sawu a cikin kwalekwale a gabar tabkin.

Amma sai aka gano ba su suke yi ba, suna loda wasu kaya ne da ba gane ko mene ne ba a ciki.

Sabanin rahoton kafafen yada labaran, sai da muka yi ta lura kafin a kai wa mayakan na ISWAP da suka yi shigar masunta hari,” inji shi. 

Hakan na zuwa ne kwanaki kadan bayan wani jirin soji ya kai wa fararen hula hari bisa kuskure a kauyen Buhari da ke yankin Babbangida a Jihar Yobe.

Bayan tabbatar da rahoton da ya gano yadda ’yan ta’addar suka mayar da dajin maboyarsu sai da aka yi sintiri domin sake tabbatarwa ta jiragen sama inda aka gano mutanen na gudanar da harkokinsu sak da na ’yan kungiyar ISWAP,” kafin aka kai musu harin.

Onyeuko ya kara da cewa dokar haramta su a yankin na nan tana aiki, ya kuma tabbatar da cewa babu wata mata ko yara kanana a cikin wuraren da aka kai wa harin.

A cewarsa, sai da jiragen yaki suka tabbatar cewa babu yadda za a yi harin ya shafi yankunan fararen hula a yankin kafin suka kai farmakin.

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50