Mayakan ISWAP sun kashe DPO a Borno
ISWAP ta kutsa cikin New Marte da misalin ƙarfe 7:30 na yammacin ranar Litinin
Wasu da ake kyautata zaton ’yan tayar da ƙayar-baya ta ISWAP ne sun kashe wani babban jami’in ’yan sanda a yankin arewacin jihar Borno.
Aminiya ta samu labarin cewa ISWAP ta kutsa cikin yankin New Marte da misalin ƙarfe 7:30 na yammacin ranar Litinin inda suka far wa wani ma’aikacin lafiya da ya yi sa’a ya tsere.
- Mafi karancin albashin 54,000 raunin hankali ne —’Yan kwadago
- Gwamnati ta gabatar da N54,000 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashi
- Yakin aiki: Ba gudu ba ja da baya —Kungiyoyin Kwadago
An ruwaito ma’aikacin lafiyar ya garzaya ofishin ’yan sandan domin sanar da su.
A lokacin da aka kira shi a waya, babban jami’n ofishin ’yan sandan yankin (DPO) ya bi sawun ’yan tada kayar bayan, amma abin takaici sai suka yi wa ayarin ’yan sanda kwanton bauna.
Wata majiyar tsaro ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce a ranar Litinin ne mayakan suka shiga New Marte inda suka kashe DPO tare da raunata wasu biyu.
Wata majiya daga ’yan banga ta ce, “Wallahi abin takaici ne. Har muka rage masa hanya daga lokacin da muke komawa Dikwa a ranar. Ya ce zai ga iyalansa a Maiduguri.”