Lukurawa sun kashe mutum 17 a Kebbi
’Yan bindiga da ake zargin Lukurawa ne sun kashe mutum 17 a wani hari da suka kai a garin Mera da ke Karamar Hukumar Augie a Jihar Kebbi
’Yan bindiga da ake zargin Lukurawa ne sun kashe mutum 17 a wani hari da suka kai a garin Mera da ke Karamar Hukumar Augie a Jihar Kebbi a ranar Jumu’a domin satar shanu.
Wani da ya nemi a sakaya sunansa ya ce mutanen sun shigo garin Mera da misalin karfe 1 na dare suka saci shanun mutane da yawa.
A nan ne mutane suka yi kokarin kwato dabbobin, inda a harbin mai uwa da wabi suka kashe mutum 17, wandanda aka yi wa 15 daga cikinsu Sallah a lokaci guda a ranr Asabar.
Ganau din ya kara da cewa daga bisani aka ga gawar mutum biyu, inda su ma aka yi masu sutura aka kai su makwancinsu.
- Tsadar kayan abinci da rashin tsaro a Arewa abun damuwa ne —Sanata Babangida
- Dalilin da ke hana ci gaban noma a Nijeriya — Suleiman
- Hanyar Saminaka: Shekara 14 ana ware kuɗin gyara, amma kamar an shuka dusa