Mayar da kayan zalunci ne tushen adalci (5)

Daga Abdulkarim dayyabu Dubi yadda mu shugabanninmu na yau ke mayar da dukiyar al’umma a matsayin gadon danginsu da abokansu da aminansu da kawalansu da munafukansu da matansu da kuma ’ya’yansu. Dubi yadda suke fakewa da kwangilolin coge don azurta kansu daga dukiyar al’umma, ba tare da bin ka’idar shari’a ba. Haka kawai an san […]

Mayar da kayan zalunci ne tushen adalci (5)
Mayar da kayan zalunci ne tushen adalci (5)

Daga Abdulkarim dayyabu

Dubi yadda mu shugabanninmu na yau ke mayar da dukiyar al’umma a matsayin gadon danginsu da abokansu da aminansu da kawalansu da munafukansu da matansu da kuma ’ya’yansu. Dubi yadda suke fakewa da kwangilolin coge don azurta kansu daga dukiyar al’umma, ba tare da bin ka’idar shari’a ba. Haka kawai an san mutum bai cancanci matsayi ko mukami ba, amma sai a ba shi domin a ba shi damar handama da babakere. A lokacin da masu albashi ke cewa bai ishe su ba, ballantana ’yan fansho, amma mutum ba shi da komai kafin ya hau mulki, cikin shekara hudu kacal, sai a gan shi da kudi da kadarorin da albashinsa da alawus dinsa na shekara 40 ba su kai su iya tara masa wannan dukiyar ba. Ga shi kuma an san ba dan kasuwa ba ne, balantana a ce ribar kasuwancinsa ne. In kuma daga baya ya fara kasuwancin, to, a ina ya samu jarin? Ko kuma wane ne ya ranta masa jarin? Amsa kawai masu mukami da tawagarsu tamkar ganima ko kayan tsintuwa suka mayar da dukiyar talakawa. Don haka suke watanda da wawaso ta hanyoyi iri-iri, suna rabawa a tsakaninsu. Su kuwa talakawa ko oho, an bar su da hamma da mika da tsaki da kuma sumbatun zafin talauci da radadin fatara.
Irin wadannan shugabannin na yau, ko suna aman Ba-Sin-Mi’ara, suna kashin Sin-Wau-Ra-Takuri, saboda malanta  ko suna aman kamus da Kundin Bayanai (Encychlopedia) da Kwamfuta saboda Ingilishi, matukar sun bar tafarkin adalan shugabanni irin su Umarul Faruk, to, ko suna ganin sun sha a duniya, tabbas su tanadi haduwarsu da Allah Ta’ala a gobe kiyama. Kowag gyara ya sani, kuma kowab bata ya sani.
Umarul Faruk daya ne daga cikin wadanda aka yiwa bushara da Aljannah tun a nan duniya. Kuma shi ne Annabi (SAW) yake cewa, “Da za a yi wani Annabi a bayana, to da Umar ne.” Sannan shi ne sahabbai ke yi masa kirari da fitilar ’yan Aljanna. Amma yakan sanya hannunsa a kan wuta yana cewa dan Khaddabi za ka iya jure wannan azabar? Don kawai ya zama cikin taka-tsantsan da duniya da kuma amanar shugabancin da ya rataya a wuyansa.
Shi shugabanci ko wakilci ko alkalanci ko kuma waziranci da na’ibanci, dukkansu suna bukatar mutane adalai fiye da sauran nauye-nauye na al’umma. Komai ilimin addinin mutum, komai ilimin bokonsa, matukar bai siffantu da dabi’un adalci ba, to bai cancanci ya jagoranci mutane ko ya wakilce su ba, musamman shugabantar dukiyoyinsu da mutuncinsu da addininsu da sauran harkokin rayuwarsu baki daya.  Me za a yi da irin shugabanninmu na yau a kasar nan? ’Yan boko sata! Siyasa damfara! Addini yaudara! Illarsu ce ta dagula komai, ta rikita kowa, kuma ta sakwarkwatar mana da rayuwa. Sun rusa shugabanci, sun lalata ilimin boko. Sun gurbata siyasa. Sun munafinci addini. Sun kuma cuci al’umma.
Saboda haka dole ne mu dawo daga rakiyar ’yan boko tsura, ba tare da hadi da nagarta ba. Da kuma ’yan addinin baka, ba tare da aiki da shi ba. Wato wadanda suke waliyai a baki, amma shaidanu ko fir’aunoni a zuciya. Ya kamata mu lalubo mutane managarta a furuci da aiki da kuma zuciya. Irin su ne kawai za su iya kawo gyara da ci gaba a dukkan fannonin rayuwarmu. Irin su ne za su iya fitar da kasar nan daga kangin da take ciki na lalacewar komai da kowa.
Duk wata kasa ko wata al’umma, da aka ga ta cimma burinta, ko ta kai ga daukaka, ko kuma ta kai ga samun nasara a abubuwan da ta sanya a gaba, to adalcin shugabanninsu ne ya kai su ga haka. Dubi kasashe kamar Afirka ta Kudu da Ghana da China (Sin) da Indiya da Iran da Saudiyya da makamantansu. Duk wadannan kasashe ba tarin mukamin boko na sakandare ko diploma ko digiri ko mastas ko dokta ko kuma farfesa ne ma’aunin zaben shugaba ko fitar da shi ba a wurinsu. Duk kasashen da suka san me suke yi, suna binciko mutane ne adalai managarta, masu asali, gogaggu, kuma kwararru a sabgar fafutikar neman ’yanci ko gwagwarmayar yakar zalunci, ko gudanar da shugabnci domin su shugabance su, ko kuma su wakilce su a duk wata gaba ta jagorancin al’umma, ko kula da dukiyoyinsu, ko bunkasa addininsu, ko kuma kyautata rayuwar jama’arsu.
Dubi yadda Afirka ta Kudu ta samu ci gaba a karkashin jagorancin Nelson Mandela. Dubi shugabansu na yanzu, Jacob Zuma wanda koda firamare bai yi ba, amma shi suka zaba saboda nagartarsa da gogewarsa. Kai mafi yawan mutanen da suka cimma nasara a shugabancinsu da wakilcinsu, ba mutane ne wadanda suke tutiya da kwalin satifiket na jami’o’i da kwalejoji ba ne. Mutane ne wadanda suke da kyakkyawar shaidar nagarta da fafutuka da gogewa a hulda da jama’a da sanin matsalolinsu da kuma kwarewa a sanin hanyoyin kawo gyara da canji.
Wannan kan iya kasancewa ne kawai idan aka samu wayayyun talakawa irin na lokacin su Malam Aminu Kano, wadanda suka san darajar ’yanci da martabar adalci. Irin wadanda suka yi gwagwarmayar fatattakar Turawan mulkin mallaka daga kasan nan, har ta samu ’yanci. Sannan suka yi fafutikar kawar da mulkin sarakuna, wanda ya gurbata da zalunci da danniya. Kuma suka yi tsayuwar daka don ganin shugabanci ya dawo hannu ’ya’yan talakawa.
Yau ga shi mulkin na hannun ’ya’yan talakawa, amma su ke gallaza wa iyayensu da ’yan uwansu talakawa. Sun bar asalin sanadiyar da aka yi fafutikar mulkin ya dawo hannunsu. Yau su ma ga su sun zama manyan azzalumai, mahandama, barayin gwamnati, kuma ’yan koren sarakuna da tsofaffin sojoji da manyan attajirai da sunan boko ko siyasa ko addini. Kai har ma warwason sarautun gargajiya suke yi don su samu daurin gindin mike kafa da kuma ci gaba da aiwatar da tabargazarsu ko don kare abin da suka wawura daga dukiyar al’umma ta haramtacciyar hanya.
Ganin yadda masu mulki suka dauki talakawa yau a matsayin kidahumai kuma shashashu, ya sanya kowane mutum, koda kuwa mara asali ne, ko barawon gwannati ne, ko fajiri ne fasiki, ko azzalumi ne mahandami, ko kuma ja’iri ne munafuki, kawai sai ya wanke kwaurinsa ya dauko jakar kudi, ya shigo siyasa, don ya nemi damar ci gaba da barnarsa ta amfani da lasisin mulki.
Su kuwa rubabbun talakawa, babu ruwansu da wane ne zai mulke su, matukar za su samu abin lasawa, komai kankantarsa. Koda kuwa ba zai ishe su cefanen mako ko wata ba.
Da kuwa managarta kuma wayayyun talakawa za su dake, su yi aiki tukuru, da sun wayar da kan sauran al’umma, kan kada su yarda su sayar da ’yancinsu da na iyaye da kakanninsu da na jikoki da ’ya’yansu da rashawar kudin siyasa, koda kuwa kudin sun kai Fam taba sama ne. Saboda ’yanci da shugabannin kwarai, sun fi duk abin da mutum yake zaton zai samu, a fannin kawo gyara da samar da yalwar arziki da kuma samun zaman lafiya.

Abdulkarim daiyabu
Shugaban Rundunar Adalci ta Najeriya
   08060116666, 08023106666