Mayar da matukan jirgi malaman makaranta a Kano
La’akari da rahoton da aka samu, cewa hazikan matasa maza da mata su 100 da Gwamnatin Jihar Kano ta dauki nauyin tura su kasashen waje, suka koyo sana’ar tukin jirgin sama suka bige da aikin koyarwa a makarantun gwamnatin jihar, maimakon sana’ar da suka kware kanta, za mu iya cewa wannan abin takaici ne ga […]
La’akari da rahoton da aka samu, cewa hazikan matasa maza da mata su 100 da Gwamnatin Jihar Kano ta dauki nauyin tura su kasashen waje, suka koyo sana’ar tukin jirgin sama suka bige da aikin koyarwa a makarantun gwamnatin jihar, maimakon sana’ar da suka kware kanta, za mu iya cewa wannan abin takaici ne ga ita kanta gwamnatin jihar da ma al’ummar Najeriya baki daya.
A watan Maris, 2013 ne gwamnati zamanin mulkin tsohon Gwamna Rabi’u Musa Kwankwaso ta ware kimanin Naira biliyan 1.1 (Dala miliyan 6.7) a matsayin tallafin karatu na musamman ga matasa 100 daga jihar, inda aka tura su wani kwas na watanni 18, a makarantar koyon tukin jirgin sama da ke birin Amman na kasar Jordan.
Matasan nan 85 ne suka kammala kwas din, a yayin da 82 cikinsu, suka dawo gida. A ka’ida, kamata ya yi a tura su zuwa Zariya, Kwalejin Koyon Tukin Jirgi, domin su yi wani takaitaccen kwas na samun shaidar tukin jirgi. Maimakon haka, sai gwamnati ta mayar da su ma’aikatanta, ta tura wasu daga cikinsu zuwa makarantu a matsayin malaman makaranta, wasu kuma ta raba su zuwa wasu ma’aikattu, a matsayin ma’aikatan ofis. Kamar yadda al’amarin yake, gwamnatin jihar na da bukatar biyan makarantar Zariya, Naira miliyan 500 domin dawainiyar wannan takaitaccen kwas na matasan, don haka ganin kuncin rashin kudin shiga da gwamnati ke fama da shi, shi ya sanya Gwamna Ganduje ya jingine batun tura su can. Haka kuma, domin kada a ce an yi asarar dukiyar da aka kashe masu a baya, shi ya sa ya mayar da su malaman makaranta da ma’aikatan ofis.
A zamanin mulkinsa, Gwamna Kwankwaso ya sha yabo, yadda ya rika tura dalibai da dama zuwa sassan duniya daban-daban, domin karo karatu, yadda za su zama masu amfani ga kasa da kuma kawunansu. Sai dai kafin a yi wannan, mun yi tsammanin za a natsu tukunna, a yi nazarin irin kwasa-kwasan da za su karanto, su kasance wadanda za su amfani al’umma kuma su kasance wadanda zamani ke tinkaho da su. Ba Jihar Kano kadai ba, wasu jihohin na Arewa ma sun tura nasu matasan zuwa irin wadannan makarantu na waje, domin karo ilimi. Mafi yawan lokaci, kwasa-kwasan masu muhimmanci ne, wadanda za su kasance masu amfani ga al’ummar kasa. Kwasa-kwasan da suka hada da likitanci, hada magunguna, injiniyanci, noma da sauarnsu. Kwas din koyon tukin jirgi kuwa yana da tsada, duk da cewa muhimmi ne, kuma yana daukar shekaru kafin a kware. Kamata ya yi a ce, kafin a tura wadannan matasa 100 domin karanto wannan kwas, an yi nazari cewa, shin akwai guraben da za su yi aiki a kamfanonin jiragen sama da ake da su a kasa ko kuwa?
A yanzu haka da ake batun nan, kasar nan tana da matuka jirgin sama guda 7,103 da suka yi rijista da Hukumar Kula Da Al’amuran Zirga-Zirgar Jiragen Sama ta Najeriya (NCAA). Cikin wadannan adadi, matuka 2,093 ne kacal suke da lasisi, alhali guda 93 sun nuna bukatun sabunta nasu lasisin. Da tun farko Gwamnatin Jihar Kano ta yi la’akari da wannan ma kadai, da ba ta bata lokacinta da dukiya wajen tura matasa har 100 zuwa Jordan don nakalto wannan kwas na tukin jirgi ba.
Duk da cewa Kwamishinan Watsa Labarai na Jihar Kano, Muhammad Garba ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta kulla yarjejeniya da kamfanin Azman Air, cewa zai koyar da matasan, sannan ya dauke su aiki, amma dai abu ne mai wuya kamfanin ya iya ba dukkansu aikin yi. Don haka an baro shiri tun rani, domin kuwa ba a yi zuzzurfan tunani ba tun da farko, da ba a tura su wannan kwas ba.
Haka kuma, matakin da aka dauka a yanzu bai dace ba, domin kuwa bai kamata a tura su domin koyarwa a makarantu ko kuma su zama ma’aikatan ofis ba, domin kuwa ba su koyi hakan ba, balle su kware. Duk da cewa aljihun gwamnatin ya yi kasa, amma da kamata ya yi koda ba dukkansu ba, kamata ya yi a zabi wasu daga ciki, a tura su su kammala kwas din, inda ko ba a nan Najeriya ba, idan sun kammala za su iya samun aiki a wasu kasashen na Afirika. Ko kuma a shiga yarjejeniya da su, bayan sun gama kwas din, a san hanyar da za su biya gwamnati wani kaso na kudin da aka kashe a kansu, wanda haka ake yi a wasu kasashe da suka ci gaba na duniya.
A nan, muna ba Gwamnatin Jihar Kano da sauran gwamnatoci shawara, cewa su rika yin taka-tsan-tsan a duk lokacin da za su aiwatar da wani kuduri da ya shafi al’umma kamar wannan. Kada a rika yin abu ido rufe da nufin samun yabo a siyasance, alhali abin ba zai haifar da alfanu ga al’umma ba, musamman ma irin wannan, inda ake tura matasa da yawa zuwa karatu kasashen waje, ba tare da la’akari da matsalar da hakan za ta haifar ba daga bisani