Mayar da mu saniyar ware ya sa muka kafa kungiyarmu – Galadimawa

Shugaban kungiyar APC Hausa Fulani Malam Sanusi Zubairu Galadimawa, ya ce mayar da al’ummar Hausa Fulani saniyar ware a Babban Birnin Tarayya Abuja ne ya sa suka kafa kungiyar. Shugaban ya bayyana hakan ne lokacin da suka kawo wa jaridar Aminiya ziyara tare da jami’in yada labaran kungiyar kuma shugaban matasan jam’iyyar reshen Tsakiyar Birnin […]

Mayar da mu saniyar ware ya sa muka kafa kungiyarmu – Galadimawa
Mayar da mu saniyar ware ya sa muka kafa kungiyarmu – Galadimawa

Shugaban kungiyar APC Hausa Fulani Malam Sanusi Zubairu Galadimawa, ya ce mayar da al’ummar Hausa Fulani saniyar ware a Babban Birnin Tarayya Abuja ne ya sa suka kafa kungiyar.

Shugaban ya bayyana hakan ne lokacin da suka kawo wa jaridar Aminiya ziyara tare da jami’in yada labaran kungiyar kuma shugaban matasan jam’iyyar reshen Tsakiyar Birnin Abuja, Yusuf Musa Musawa, kwanakin baya.
“An kafa wannan kungiyar ce a bara. Mun kafa ta ne domin nema wa al’ummar Hausa Fulani da ke zaune a Babban Birnin Tarayya Abuja ’yanci da kuma dama gwargwadon gudunmuwar da muke bayarwa,” inji shugaban.
Daga nan ya kara da cewa mutane da dama ba su fahimci cewa akwai al’ummar Hausa Fulani da masu yawan gaske ba a Abuja. “Muna da kusan kashi 65 cikin 100 na jama’ar da suke kada kuri’a. Tarihi ya muna cewa babu wanda ya riga Bahaushe zuwa Abuja. Muna da mambobi da sukai fiye da mutum 300. Muna da fatan cewa tunda mun taimaki ’yan kasa saboda haka muke ganin mu ma yakamata a dafa mana domin akalla a cewa yau muna da shugaba akalla guda na karamar hukuma. Cikin kananan hukumomin nan guda shida da ake da su a Abuja, yakamata a ce muna da shugaban karamar hukuma guda daya ko biyu musamman ma na tsakiyar birnin Abujan,” inji shi.
A karshe ya ce babban dalilin da ya sa suka kungiyar shi ne su wayar wa da jama’arsu kai “su daina cewa sai wane, sai wane. Lokaci ya yi da mu ma za mu fito, mu yanki fom domin tsaya wa takarar shugabanci kamar kujerar shugaban karamar hukumar Abuja Municipal.”