Maza ne babban kalubale ga siyasar mata a Najeriya -Honorabul Khadija Ibrahim

Hajiya Khadija Abba Ibrahim wacce aka haifa a shekarar 1967, tana daya daga cikin fitattun matan da ake alfahari da su a Arewa, kasancewarta ‘yar Majalisar Wakilai kuma ‘yar siyasa da tauraruwarta ke haskawa a fagen siyasar Najeriya. Mafi akasarin karatunta ta yi ne a kasashen waje, inda ta samu takardun shedar kammala karatun Kwaleji […]

Maza ne babban kalubale ga siyasar mata a Najeriya -Honorabul Khadija Ibrahim
Maza ne babban kalubale ga siyasar mata a Najeriya -Honorabul Khadija Ibrahim

Hajiya Khadija Abba Ibrahim wacce aka haifa a shekarar 1967, tana daya daga cikin fitattun matan da ake alfahari da su a Arewa, kasancewarta ‘yar Majalisar Wakilai kuma ‘yar siyasa da tauraruwarta ke haskawa a fagen siyasar Najeriya. Mafi akasarin karatunta ta yi ne a kasashen waje, inda ta samu takardun shedar kammala karatun Kwaleji da Difiloma a Makarantar Headington da Kwalejin Padworth da ke Birtaniya. Sannan ta samu digiri a fanni cinikayya a Jami’ar Surrey da ke Birtaniya. Hajiya Khadija ta zama wakiliyar Mazabar Damaturu da Gujba da Gulani daTarmuwa da ke Jihar Yobe a shekarar 2007 inda har yau take kan kujerar. Kafi nan, ta rike mukamai da dama ciki har da Kwamishina a Jihar Yobe daga 2004 zuwa 2007. A hirar da gogaggiyar ‘yar siyasar ta yi da Zinariya, ta koka game da kalubalen da mata ke fuskanta a harkar siyasar Nijeriya. Ga yadda hirar ta kasance:

Hajiya ki gabatar mana da kanki.

Sunana Khadija Bukar Abba Ibrahim, ina wakiltar Damaturu da Gujibagulani daTarmuwa a majalisa karkashin jam’iyyar APC.
Kun kammala aiki a Majalisa ta bakwai ga shi cikin hukunci Ubangiji kin dawo an fara Majalisa ta takwas da ke, shin wace gudummawa ce mata suke bayarwa a siyasance?
Lallai mata suna ba da gudumawa ba kadan ba, kuma sun taka rawar gani tun ma musamman a wannan lokacin don in aka duba a kashi dari, kashi hamsi mata ne suka fito kwansu da kwarkwatansu don ganin mun yi nasara. Don haka ina ganin ya cancanta a bai wa mata mukamai masu dama a majalisa da fannin zartarwa na gwamnati a ko’ina a kasar nan.
Ganin cewa a Majalisa ta takwas mata 24 ne wakilai amma a wannan karo kuma sai matan suka ragu zuwa goma sha shida, wace matsala ce ta haddasa hakan?
A gaskiya an samu ci baya kuma ba komai ya haifar da hakan ba illa mazan ne ba su baiwa mata dama. Kamar yanda na ce a baya, mata ne suka fito da dama don tabbatar da wannan zaben wanda ya kamata a ce an yi masu sakayya ta hanyar zaban mata wadanda suka tsaya takara, amma maza suna dagewa har ma da fada inda a gaskiya in mace ce ba za ta iya ba. Ina tunawa akwai inda aka ce a Gombe ma har an kashe wani. To kin ga ire-iren wannan mata ba za su iya ba. A ganina siyarsa ta kara baci inda in mace ta samu kanta a wannan yanayi ba za ta iya ba. Kuma a wasu wuraren a kan cewa mata su janye su bar wa namiji. Saboda haka ina gani akwai tafiya sosai a gabanmu mata a siyasance.
Kin yi bayani a kan dalilan da suka janyo karancin mata a siyasa amma, wasu za su ce wadanna hujjojin ba su da kwarin tsorata mata a siyasa.
A gaskiya abin tsoro ne kuma yawancin mu mata ba za mu iya fito-na- fito don siyasa ba saboda irin baiwar da Allah Ya yi mana, kin ga ke nan ana tafiya gaba wata rana maimakon matan su karu za su janye gaba daya. Sai dai in mazan su ne za su tsaya su taimaka su ga su ma sun tura mata gaba ko kuma a tsara wata doka da za ta bai wa mata kason mukamai. Misali a ce doka ta tsara cewa a mukaman siyasa mata ne za su cike kashi talatin da biyar, sabanin da muke da kashi takwas yanzu a wannan karo an dawo kashi hudu. In ba haka a ka yi ba yawanci maza ba za su yarda su sakewa mata mukamai ba, sai dai kawai in abin ya fi karfin su.
To mene ne mazan suka fi matan a wannan fanni, kwarewar siyasa ce ko kuwa me?
Kawai dai yadda tsarin al’adunmu ya ke da kuma yadda tunani yake a kan mace. Sai ki ji ana cewa ai wannan mukami bai dace da mace ba ko kuma bai kamata mace ta rike waccan wuri ba. Amma in kika duba kasashen duniya da suka ci gaba za ki ga cewa mata da dama suna ba da gudumawa wajen shugabanci da zartarwa. Ba su raina gudumawar mace ko kuma a ce mace ba za ta iya ba.
Wace irin rawa kudi ke takawa a siyasar Nijeriya?