Maza sun sanya hijabi a Iran don hana tursasa wa mata sanya hijabi

A makon da ya gabata ne mazan Iran saka yi ta nuna hotunansu sanye da hijabi a shafukan sadarwa na intanet, inda sukan hadu da matansu ko ’yan uwansu mata, wadanda ba su lullube gashinsu ba, don nuna adawarsu da dokar tursasa wa mata sanya hijabi.Rukunin mazan na adawa ne da tursasa wa mata sanya […]

Maza sun sanya hijabi a Iran don hana tursasa wa mata sanya hijabi
Maza sun sanya hijabi a Iran don hana tursasa wa mata sanya hijabi

A makon da ya gabata ne mazan Iran saka yi ta nuna hotunansu sanye da hijabi a shafukan sadarwa na intanet, inda sukan hadu da matansu ko ’yan uwansu mata, wadanda ba su lullube gashinsu ba, don nuna adawarsu da dokar tursasa wa mata sanya hijabi.
Rukunin mazan na adawa ne da tursasa wa mata sanya hijabi a kasar Iran. Kuma lamarin ya samo asali ne tun sa’adda wata ’yar jarida mai fafutikar hakkin al’umma, Masih Alinejad da ke zaune a birnin New York ta Amurka da su tallafa wa matar da lakabin fafutikar “Hakkina da aka tauye – My Stealthy Freedom.” Tun bayan juyin juya halin Iran na shekarar 1979, ya zama dole ga mata su lullube gashin kansu. Matan da ba su yi lullubi da hijabi ba, ana daukarsu a matsayin fetsararrun da ke bayyana gashinsu da fuskarsu; saboda haka ake yi musu tara ko hukuncin dauri.
A shafinta na facebook, Alinejad ta baje hotunan matan Iran da ke jin dadin “’’yanci, ta hanyar cire hijabi a wajen gidansu. Yanzu kuma ta bukaci maza su tallafa wa fafutifkarta, ta hanyar sanya hijabi a kansu tare da mata marasa hijabi.
Mutanen da suka yi wa Alinejad sharhi a shafinta, mafi yawansu sun goyi bayan wannan fafutika, tare da karfafa gwiwar mata su nemi ’yancinsu.
Sharhin Linda berstraten cewa ta yi: “A kyale maza da mata su zabi yanayin rayuwar da suke son gudanarwa, da kuma tsarin tufafinsu. Al’amarin na da kayatarwa ganin yadda maza suka goya wa matan baya a wannan fafutikar ta ’yanci da daidaito!”
Jariar Gufews ta ruwaito labarin tare da baje hotunan mazan da ke goyon bayan fafutikar daina tursasa wa mata sanya hijabi a kasar Iran.