Mazan ne ko matan a tsakanin Hausawa?

Mako goma sha daya muka dauka muna tattaunawa bisa batutuwan da wata baiwar Allah ta turo mini ta akwatin ajiye sakona a Intanet, na kuma ba ta dama ta amaye kusan dukkan abubuwan da suka dame ta game da yadda ake kallon matan Hausawa da irin dangantakar da ke tsakaninsu da mazajen Hausawa. Tattaunawa ce […]

Mazan ne ko matan a tsakanin Hausawa?
Mazan ne ko matan a tsakanin Hausawa?

Mako goma sha daya muka dauka muna tattaunawa bisa batutuwan da wata baiwar Allah ta turo mini ta akwatin ajiye sakona a Intanet, na kuma ba ta dama ta amaye kusan dukkan abubuwan da suka dame ta game da yadda ake kallon matan Hausawa da irin dangantakar da ke tsakaninsu da mazajen Hausawa. Tattaunawa ce da na samu karin haske game da rayuwar mata da iliminsu da tattalin arzikinsu da zamantakewarsu. Tun kafin na mayar da nawa martani daruruwan mutane suka zaku su shiga cikin zancen ko takaddamar, da yake na ce zan tofa albarkacin bakina ni ma, sai na ga ya fi dacewa na ba wasu dama su ce wani abu tunda har sun fara cewar. Abin da za mu yi ke nan a wannan makon in sha Allah. A sha karatu lafiya.
 
ASY Kano:
Wannan labari wala-alla kirkirarre ne ko samamme ya ilimantar kwarai da gaske. Amma ni gaskiya na fi jibanta lamarin yin kulle na Malam Bahaushe akan dadaddiyar al’ada wadda ba ta da adalci ko kadan, wannan al’ada wadda sam ba ta da nasaba da addini ko kadan….Kashi 70 na mazajen Hausawa sun dauki mace ma’aikaciya ko ‘yar kasuwa ko wani aiki da ake cudanya da maza a matsayin mai babban laifi kuma marar kamun kai. Wannan bakar akida ta taimaka gaya wajen bakin talauci da jahilci da yankin Arewacin Najeriya yake fama da shi a halin yanzu idan muka yi la’akaci da yankin Kudu inda mata ke gogayya da mazaje a makarantu da ayyukan ofis da kasuwanni. Kai hasali ma a garuruwa irin Legas mata sun fi yawa a kasuwanni a harkar saye da sayarwa…to fatarmu ita ce mu ma mu ilimanta mu ajiye al’adu marasa tushe a addini.
 
Tamim Harun:
Ina Addu’a Allah Ya kara wa Malam lafiya da tsawon rai, ya yi wa zuriya albarka. Wannan matsala ba ta mazan Hausawa ba ce ko matan Hausawa, matsala ce ta al’umma, musamman mutanen Afirka, amma tunda ana magana game da Hausawa, to, wannan matsala tana bukatar ilimi na addini da zamani, sannan a san bambacin addini da al’ada da kuma bambacin gaskiya da son zuciya. Amma akwai aiki a gaban malamai da dalibai, Allah Ya yi musu jagoranci da mu baki daya.
 
Sagir Musbahu Daura Dole:
Lallai wannan mata ba karamar ’yar takife ba ce, domin tun farkon wannan mukala take kutubol da tunanina amma yau an zo wajen! Don haka kafin dai na yi wani dogon tsokaci ko nazari, bari na sake makalewa a gefe in zuba na mujiya har sai Malam ya kammala nasa nazarin da martanin “Mazan Ko Matan,” lallai nan ma za mu kwashi romon ilimi da fahimtar inda wannan mata ta sanya gaba, fatarmu Allah Ya karawa Malam lafiya da juriya tare da mu baki daya.
 
Aliyu Muri:
Bismillahi! Tabdi jam! Wato ni a tawa fahimtar duk kanwar ja ce. Zama muke irin na ’yan marina kuma kowa na neman sa’ar kowa, kuma kowa bai san asirin kowa ba har ila yau dai kowa idonsa ya rufe wajen neman abin duniya ba neman abin rufin asirin junansu ba! Rashin tuna baya ne kawai ya haifar da wannan ka-ce-na-ce, wato lokacin da iyayenmu mata da iyayenmu maza ke tausayin juna da taimakon juna kuma kowanensu wajen nema da ci da gumi suke tsaye kamar hakori.
Saboda muhinmancin tarihi zan ja hankalinmu zuwa shekaru kimanin arba’in ko fi da suka wuce lokacin muna yara ga masu shekaru irin namu. A wancan lokacin ni dai a iya sanina a layinmu wanda ke da gidaje masu yawa da wuya a samu wani gida a cikinsu da matan gidan ko mazan gidan ba sa yin sana’a kuma maza da mata a wancan lokacin suna zama na kaunar juna na cude-ni-in-cude-ka. Ga misali a gidanmu mahaifiyata zan iya tunawa tana yin sana’ar fankaso da miya, duk safiya. Takan yi miyar da dare haka shi ma gyara garin alkamar da take yin fankason da shi da kuma kwabinsa. Takan yi wannan ayyuka ne da dare inda take mana tatsunniya, wanda sai yanzu na gane manufarta ba komai ba ne illa mu taya ta zama yayin da take aikinta kada mu yi barci. Kuma idan gari ya waye tun bayan kammala sallar asubahi za ta fara sana’ar soya fankaso a cikin gida. Wasu masayan da zaran sun fito daga masallaci za su biyo su yi oda a sayo masu su karya kumallo a nan. Yara kuma akan aiko su daga gidaje da kwanoni su shigo gida kai-tsaye su saya. Mu ma a nan muke karyawa kafin mu tafi makaranta. Batun dai shi ne mahaifinmu bai taba kosawa da sana’arta ba, bugu da kari ma dai ita kadai ce matarsa kuma mutuwa ta raba su.
A iya sanina ban taba ganin ta yi yaji ba. Kuma a kai-a kai mahaifinmu yakan kara mata jarinta. Haka abin yake duk layinmu ba gidan da matan da ke zaune a ciki ba sa yin sana’a, walau ta ci wadda tafi yawa ko ta amfanin yau da kullum. Haka su ma mazan suke kowa da irin tasa sana’ar kuma ba aikin gwamnati ba na albashi, wato ta yau bashi, gobe rance! Sana’a wadda da zarar wata ya yi husufi albashi ya kare ba a ji alat ba maza za su zare su fara sambatu da kankanci. A irin wannan rayuwa ta yau rayuwar da mijin ko matar dayansu kan zama kaska ko kuma su duka biyun su kasance haihuwar guzuma. Me ke hana mace ta kosa da miji ko miji ya kosa da mata? Me ke hana aure ya yi ta macewa saboda dalilin da bai taka kara ya karya ba, wani ma za ka iske kan lattin dafa abinci ne ko rashin dafa shi yake sakin mata? Na tabbata yau da a ce za a yi bincike a kotunan garin Kaduna kadai inda Farfesa ke zaune dangane da matsalar aure da zai tarar cewa mafi yawan kararrakin da suka shafi aurarraki ko mutuwarsu a kotunan na matar Bahaushe ne ba na sauran matan kabilu ba! Na dora kazar karfi da neman a zabi kotuna tun daga Kawo har Kakuri kuma daga Hayin Rigasa har zuwa Hayin danmani za a tabbatar da wannan hasashen ya kasance haka idan aka bi rajistar kotunan! Babban abin lura dai shi ne yau ko fina-finan Hausa da littattafan marubutan Hausa akasarinsu jigon duk bai wuce matsalar zaman auren Bahaushe ba. Maganar dai daya ce tak ba biyu ba. Da mazan da matan a wannan zamani duk tare ta ruga! Wato dai kare kada ya rena kirar dila….! Na gode!