Mazauna Baga na fama da karancin abinci

Mazauna garin Baga da ke karamar Hukumar Kukawa a Jihar Borno, sun koka kan rashin isasshen abinci da ababen more rayuwa a garin bayan kwato shi daga hannun mayakan kungiyar Boko Haram, kuma sun ce jami’an gwamnati ba su zuwa garin don ganin halin da suke ciki.daya daga cikin garin da ya gudo zuwa Maiduguri […]

Mazauna Baga na fama da karancin abinci
Mazauna Baga na fama da karancin abinci

Mazauna garin Baga da ke karamar Hukumar Kukawa a Jihar Borno, sun koka kan rashin isasshen abinci da ababen more rayuwa a garin bayan kwato shi daga hannun mayakan kungiyar Boko Haram, kuma sun ce jami’an gwamnati ba su zuwa garin don ganin halin da suke ciki.
daya daga cikin garin da ya gudo zuwa Maiduguri mai suna Malam Bunu Abacha, ya shaida wa wakilinmu cewa yunwa ce ta koro su daga Baga zuwa Maiduguri, kuma sun mutum 500 zuwa 600 da suka gudo saboda yunwa. “Ba mu da abinci, ba mu da kudin sayan abincin, don haka muka yanke shawarar  tserewa zuwa Maiduguri, kuma mun biyo motocin da suka kai kayan sojoji ne, inda suka ajiye mu a Monguno muka kara so da kafa. Gaskiyar zance abinci ba ya shiga garin Baga, saboda jami’an tsaro sun hana shiga ko fitar da wani abu cikin garin, inda ledar taliya daya ta kai Naira 700, sai mudun shinkafa da ke kai Naira 1000 zuwa 1200.”
Malam Bunu ya ce mazauna garin suna sayen kwanon gari a kan Naira 700 zuwa 800, kuma a yanzu haka sun bar sama da mutum dubu biyar da suke fama da yunwa saboda rashin abinci da kudi, kuma ga shi sojoji sun hana shiga sun hana fita.
Malam Abacha, ya roki Gwamnatin Tarayya da ta Jihar Borno su dube su da idon rahama su bude hanyar shiga garin Baga da tare da kai musu abinci.
Sai dai Shugaban riko na karamar Hukumar Kukawa Musa Alhaji Bukar, ya musanta zargin cewa babu abinci a garin na Baga, inda ya ce, “Wannan ba gaskiya ba ne wanda ya fadi haka bai sani ba ne domin gwamnati ta sayi abinci na miliyoyin kudi ta aike wa mutanen Baga, wadanda suka fito zuwa Maiduguri ba su sani ba don haka suke ce babu abinci.”